1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matashiyar sabbin dokoki a ƙasashe masu amfani da kudin euro

January 14, 2012

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ci alwashin hanzarta garanbawul ta fuskar hada hadar kuɗaɗe a tsakanin ƙasashe masu amfani da kuɗin euro.

https://p.dw.com/p/13jq4
German Chancellor Angela Merkel gestures during her speech at the German federal parliament, Bundestag, in Berlin, Germany, Wednesday, Dec. 14, 2011. (Foto:Michael Sohn/AP/dapd)
Shugabar gwamnatin Jamus Angela MerkelHoto: dapd

Shugabannin Tarayyar Turai sun yi alƙawarin hanzarta ɗaukar matakai na samar da sabbin dokoki da za su ƙarfafa harkokin hada hadar kuɗaɗe da kuma samar da gidauniyar tallafin ceto ta dundundun. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce rage matsayin biyan bashi na wasu ƙasashen Turai da hukumar Standard & Poors ta yi alama ce dake nuni da wajibcin wakilan ƙasashen su rattaba hannu akan sabon jadawalin dokokin kuɗaɗen ba tare da wani jinkiri ba, yayin da nan ba da jimawa ba za'a samar da sabon shirin tallafin ceton tattalin arzikin wanda aka yiwa laƙabi da ESM a taƙaice. " Wannan matashiya ce a gare mu ta mu hanzarta aiwatar da jadawalin harkokin kuɗaɗe. Mu dubba dukkanin hanyoyin da suka dace na tabbatar da hakan. Wajibi ne mu ɗauki wannan ƙalubale da ƙara jan ɗamara musamman ta fuskar haraji da kuma rage kashe kuɗaɗe don samun cigaba mai ɗorewa".

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Usman Shehu Usman