1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matashiyar da ta kafa kungiyar wayar da kan zaurawa

Nasir Salisu Zango
May 30, 2018

a jihar Kano ne dai matashiyar mawakiya mai suna Asmau Sadeeq da aka fi sani da suna Baby Nice ta kafa kungiya domin wayar da kan zaurawa da su nemi na kansu da wayar musu kai bisa illolin shaye-shayen miyagun kwayoyi.

https://p.dw.com/p/2yd2G

Cikakken sunan ta shi ne Asmau Sadiq, lakabin ta kuma Baby nice, ita dai zabiya ce mai rera wakokin gada ko kuma dandali, daga bisani kuma ta rikide ta zama mai fafutukar wayar da kan mata wajen guje wa shaye-shaye da kuma neman na kai da nufin huce takaicin mazaje. Baby nice, ta ce a bangaren matan ma tafi mayar da hankali akan zaurawa da yan mata, ganin cewar sune suka dandana kadan daga cikin azabar da maza ke gana musu. In da ta ce takan wayar musu da kai akan neman abin yi, kuma da yake tace ta lura wasu lokutan takaicin mazan kan jefa su cikin dibgar miyagun kwayoyi ya sa take kokari wajen fadakar da su akan illar miyagun kwayoyin

Haifaffiyar jihar Bauchi, wacce ta rayu a birnin kKno, Asmau Sadiq ta shaida wa DW cewar sau da dama takan sami zaurawan da ke ba ta labaru na abin tausayi musamman ma akan abin da ya raba su da mazajen su. Ta ce ire-iren wadannan labarai na abin tausayi shi ne ya sa ta kudiri aniyar shiga wannan harka ta wayar da kan mata.

Asmau Sadiq ko kuma Baby nice, tace babban kalubalen da suke fuskanta shi ne rashin tallafin da za a ringa bai wa zauwaran, dan haka ne ma galibi ba kasafai suke samun yadda suke so ba. Amma duk da haka ta ce kadaran hadaran, kwalliya na biyan kudin sabulu.