Mamman Sani Usaini dan shekaru 26 da haihuwa na zama matashi na farko a Nijar da ya rungumi aikin nazari da fasahohin kimiyya ta hanyar zane zanen hotuna na barkwanci tun yana dan matsakaicin shekaru.
Sai dai matashin ya fi kauna da sha’awar kayan wasan yara na zamani da akan iya jonawa a akwatin talabijin ko kuma a wayoyin hannu na salula. Ta wannan hikimar ce ma ya kirkiro wasan da ya sanyawa suna Jaruman Sahel inda ya rika yada al’adun Nijar da yankin Sahel baki daya.
A Irin nasarorin da ya samu Usaini yace da wannan sana’a yake ci da sha da taimakawa iyalai da dangi da kuma sauran al’umma. Ya samar da shirye shirye da dama da suka hada da wadanda ake iya samu a wayar salula.
Batun kalubale kuwa Mamman Sani Usaini yace musamman samun kayan aikin da yake bukata na daga cikin matsalolin da ya fuskanta yana mai cewa duk abinda mutum zai yi idan ya sa hakuri da juriya yana iya cimma burinsa.