1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matasan Togo ne suka lashe gasar

August 29, 2012

Masu ban sha'awa da ilimantarwa da ban tausayi daga masu sauraronmu. Waɗanda aka tsara su ta yadda za su taimaka wa matasa tsara rayuwarsu don gaba.

https://p.dw.com/p/15zGz
Portrait Bouloufèi Bèwèzima Auf dem Bild ist der Gewinner des Learning by Ear-Geschichtenerzählwettbewerbs zu sehen: Bouloufèi Bèwèzima.
Bouloufèi Bèwèzima daga TogoHoto: Bouloufèi Bèwèzima

Bayan tsawon watanni na karatu da mahawara sashin Afirka na gidan rediyon DW, an sanar da sakamakon gasar ka cici-ka cici da aka gudanar. Wanda ya lashe gasar shine Bouloufei Bewezima da tawagarsa daga ƙasar Togo, a dangane da labarin fataucin yara da sanya su aikin da ya fi ƙarfinsu da ake yi a Afirka.

Iyayen yaran dai suna da 'ya'ya guda bakwai suna kuma fama da wahala wajen tarbiyyarsu. A sakamakon haka suka yi marhabin da tayin da gwaggonsu ta yi, inda tayi alkawarin renon yara maza guda biyu. To sai dai kuma a maimakon ta kula da yaran sai ta tura su zuwa Najeriya, inda aka tilasta musu aikin dole a gida da kuma gonar wasu masu hannu da shuni.

Da wannan bayanin Boulofei Bewezima yayi matashiyar labarinsa, wanda a haɗin guiwa da takwarorinsa na wata kungiyar matasa mai suna " A nous la planete" a birnin Lome ta kasar Togo ya lashe gasar Ji ka Karu da aka gudanar. An dai kammala labarin nasa tare da farin ciki. Domin kuwa yaran sun hau tudun natsira, inda suka isa gida suka haɗu da iyayensu bayan tserewa da kuma doguwar tafiyar da suka yi. A rayuwa ta yau da kullum dai ba kasafai ba ne irin wannan matsalar kan gama lafiya. "A duk shekara sai mun ga yara masu tarin yawa da kan katse karatu su runtuma zuwa Najeriya ko wani waje dabam su kama aiki, tare da fatan samun ikon sayen keken hawa ko babur ko kuma keken dinki, kamar yadda mawallafin ya nunar. Da yawa daga cikinsu su kan ɓata ba a sake jin ɗuriyarsu".

Auf dem Bild ist Loyce Maturu zu sehen. Sie ist ein Mitglied des „Zvandiri Youth Advocacy Teams“ und engagiert sich gegen Stigmatisierung und Diskriminierung HIV positiver Menschen. Das „Zvandiri Youth Advocacy Team“ hat beim Learning by Ear-Wettbewerb „Learning by Ear wants to tell your story!“ den 3.Platz belegt. Copyright: Andreas Keller Juli 2012, Harare, Simbabwe
Loyce Maturu wadda kungiyarsu ta zo na uku.Hoto: Andreas Keller

Labari ga Rediyo

Daidai da sauran labaran da suka shiga gasar, shi ma wannan labarin ya shafi matsaloli ne na rayuwa ta yau da kullum. Akasarin labaran da sashen shirin Ji ka Karu ya samu a makonnin baya-bayan nan sun jiɓanci batutuwa ne na ilimi da matsaloli na iyali da ɗaukar ciki ba da son rai ba da ma hakkin Yara da na Mata. A labarin da wata ƙungiya ta matasa mai suna "Tsanaga Jeunesse" a arewacin Kamaru ta gabatar, ta shafi wata yarinya ce matashiya da wani tsoho yayi mata ciki. A matsayi na uku kuwa an zaɓi labarin da ƙungiyar "Zvandiri Youth Advocacy" daga Zimbabwe ta turo ne. Babbar manufar da 'ya'yan ƙungiyar suka sa gaba dai shi ne yaƙi da kyamar da ake wa yara da matasa dake ɗauke da ƙwayar HIV. Rubuta wannan labari ga shirin Ji ka Karu ya taimaka musu matuka ainun wajen bayanin matsalolin da suke fuskanta a rayuwa ta yau da kullum, a cewar Loyce Maturu:"Muna fuskantar irin wannan ƙyama a makarantu, kai har ma a tsakanin dangi. Manufarmu a labarin shi ne mu yi bayani dalla-dalla a game da wuraren da yara da matasa masu ƙwayar HIV ke fuskantar ƙyama da wariya".

Batutuwan da kowa ke sha'awa

Azamar da shirin Ji Ka Karu yayi na taɓo dukkan matsaloli na rayuwa ta sanya shirin yayi farin jini a duk faɗin Afirka. Batutuwa dabam-dabam da masu sauraro suka aiko na masu yin nuni ne da cewar har yau akwai sauran labaran dake buƙatar a watsa su. Gaba ɗaya labarai talatin da shida aka aiko daga ƙasashe goma sha biyar dake sassa daban-daban na Afirka. Alkalai biyar daga sashen Afirka na Deutsche-Welle, da suka haɗa da Zainab Mohammed Abubakar ta Sashen Hausa, suka yi bitar labaran. Ta ce ta yi fama da wahala wajen zaɓen labarin da ya fi cancanta, saboda ƙyawawan labarai masu yawa dake akwai. Sai dai kuma duk da haka a ganin editar ta Sashen Hausa labarin da aka zaɓa shi ne ya fi cancantar cinye gasar. " Domin kuwa wannan matsalace dake da muhimmanci ga matasa ta la'akari da fataucin Yara da ake yi a ƙasashe da dama na Afirka, musamman ma idan muka lura da irin fafutukar da talakawa marasa galihu ke yi wajen kyautata makomar jin daɗin rayuwarsu".

Juli 2012, Goma, RDC Auf dem Bild sind einige Mitglieder des DW-Hörerclubs aus Goma zu sehen, die 2012 am Learning by Ear-Geschichtenerzählwettbewerb teilgenommen haben. Copyright: Alain Maboko, Vorsitzender des Clubs
Wasu matasa da suka shiga gasarHoto: Alain Maboko

Karin ilimi akan wasan kwaikwayo ga masu nasara

Labarin da ya cinye gasar daga Togo zai samu shiga cikin sabuwar salsalar shirin Ji Ka Karu da za a gabatar a shekara ta 2013. A baya ga haka a haɗin kai da mawallafan labarin, tawagar shirin Ji Ka Karu zata shirya wasan kwaikwayo ga wannan labari domin gabatarwa a Lome mazaunin Bouloufei Bewezima.

Kuma dai ko da yake labari ɗaya ne zai iya cinye gasar, amma shi ma labarin ƙungiyar "Zvandiri Youth Advocacy Teams", wanda yayi na uku, ya burge ƙwarai da gaske, kana kuma ƙungiyar na shirin gabatar da wasan kwaikwayo akan labarin game da HIV a birnin Harare.

Mawallafa: Christine Bukania da Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Umaru Aliyu