1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Yiwuwar shiga yajin aikin gama gari a Kenya

Zainab Mohammed Abubakar
June 21, 2024

Masu zanga-zanga a Kenya sun kira da a shiga yajin aikin gama-gari daga ranar 25 ga watan Yuni, domin nuna adawa da shirin kara harajin da gwamnati ta yi.

https://p.dw.com/p/4hNCO
Hoto: LUIS TATO/AFP/Getty Images

Wannan mataki na zuwa ne bayan zanga-zangar da akasarinsu matasa suka yi a wannan makon a fadin kasar Kenya.

Wata sanarwa da masu zanga-zangar suka yi ta yadawa ta yanar gizo, na kira ga daukacin al'ummar kasar ta Kenya da su fito kwansu da kwakwatarsu dopn nuna adawa da makain gwamnatin Nairobi, ta hanyar shiga yakin aikin na gama gari.

Gwamnatin Shugaba William Ruto ta kasar da ke fama da karancin kudade dai ta amince a ranar Talatar da ta gabata cewa za ta dubi yiwuwar yin gyara-gyare ga tsarin harajin, bayan arangamar da ta wakana a tsakanin wasu daruruwan matasa da jami'an 'yan sanda a Nairobi babban birnin kasar.

Sai dai kuma alamu na nuna cewa gwamnatin ta Kenya, za ta ci gaba da wasu kare-kare a kan wasu haraje-haraje, a kokarinta na rage yawan basuka da take karbowa daga ketare domin matsalolin cikin gida.