1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matan Najeriya sun shiga tsaka mai wuya a Saudiyya

September 26, 2012

Hukumomin Saudi Arabiya sun tsare mata mahajjata kusan dubu 'yan Najeriya bisa zargin ba su je da muharrammai ba.

https://p.dw.com/p/16FHr
Wer hat das Bild gemacht?:Aminu Abdullahi Wann wurde das Bild gemacht?:26.09.12 Wo wurde das Bild aufgenommen?:Saudi Arabien Bildbeschreibung: Bei welcher Gelegenheit / in welcher Situation wurde das Bild aufgenommen? Wer oder was ist auf dem Bild zu sehen? Pilgerinnen aus Nigeria in Saudi Arabien
Hoto: DW

Hukumomin Saudi Arabiya na cigaba da tsare mahajatta mata daga Najeriya a filayen jiragen Jedda da Madina.Matan sun gudanar da wata zanga-zangar lumana domin tilasta ma hukumomin ƙasar Saudiya yanke hukunci akan makomarsu.

Har yanzu hukumomin na Saudia basu ce ma matan su fiye da ɗari 900 ufan.

Tun kammala sallar subahin ta safiyar Laraba ne maniyatan mata 'yan Najeriya dake tsare a hannun hukumomi Saudiya a filin jirgin saman Jedda suka gudanar da wata zanga-zanga ta lumana, inda suke neman bayani akan makomar niyar su ta aikin hajji daga hukumomin. Wanda bayan ɗaukar lokaci jami'an ƙasar ta Saudia suka lallashi matan su fiye da 900 da su basu awowi biyar za su ji sakamako, to har yanzu bata canza zane ba.

Thousands of Moslems attend the Friday prayer at the Great Mosque of the Haram Sharif in Mecca, Saudi Arabia, on 12 November 2010 as hundreds of thousands of pilgrims pack the area to take part in the annual Hajj (pilgrimage to Mecca). Reports state that around three million Moslem pilgrims are expected to attend this year. EPA/YAHYA ARHAB +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/dpa

Na tuntuɓi wata daga cikin matan dake tsare ta wayar salula wadda tace har yanzu hukumomin na Saudia basu ce uffan ba:

Wannna lamarin ya shiga kwana na biyar da soma tsare maniyata aikin hajji mata, daga BNajeriya sabili da rashin mazajensu ko muharrammansu a tafiyarsu ta aikin hajji, kuma malam Yusuf Yahaya Alibawa, na daga cikin waɗanda suke ta ƙoƙarin gayawa hukumomin Najeriya halin da ake ciki.

Wasu maniyata da suka zo sane da irin matsalolin da sauran mata a Najeriya suka faɗa sun yi ƙoƙarin ceto wasu, amma duk da hakak wasu da yawa na cigaba da shiga hannun hukumomin Saudiya.

Muslim pilgrims pray on a rocky hill called the Mountain of Mercy, on the Plain of Arafat near Mecca, Saudi Arabia, Thursday, Nov. 26, 2009. (AP Photo/Hassan Ammar) BdT Pilger in Saudi Arabien
Hoto: AP

Tuni sauran maniyata daga johihi da dama na Najeriya suka cigaba da bayyana damuwarsu akan wannna lamari.

Mawallafi: Aminu Abdullahi
Edita: Yahouza Sadissou Madobi