Matan Masar sun shiga zanga-zanga
December 21, 2011Dubban mata a kasar Masar sun fantsama a dandalin Tahrir da ke a birnin Alƙahira domin nuna ɓacin ransu dangane da cin zarafin da jami'an tsaron suka yi wa wata mata a lokacin zanga-zanga. Matar wacce 'yan sanda suka riƙa ja a ƙas wadda kuma suka yi wa kusan tsirara an yi ta baza bidiyonta da hotunanta a gidajan telbijan na duniya. Sakatariyar harkokin wajen Amirka Hilary Clinton ta bayyana takaicinta tare da yin Allah wadai da abin da ya faru. Sannan kuma ta yi kira ga hukumomin soja da su mutunta 'yanci walwala na jama'a.
Matan sun gudanar da zanga-zanga ne duk kuwa da cewar majalisar ƙoli ta mulkin sojin ta nemi ahuwa akan abinda ta kira kuskure. Kawo yanzu dai mutane guda 14 suka rasa rayukansu a cikin boren da jama'ar suke yi na neman ganin sojojin sun gaggauta miƙa mulki ga farar hula.
Mawallafi:Abdourrahamane Hassane
Edita: Halima Balaraba Abbas