Mata a kasar Afghanistan sun kwashi tsawon shekaru 20 cikin nitsuwa da kwanciyar hankali amma labarin yiyuwar dawowar Taliban kan mulki, ya sa cikinsu ya duri ruwa bisa fargabar kwacewar 'yancin da suke da shi tun bayan girke rundunar sojan Amirka da ke sama wa kasar tsaro.