1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bunkasa ilimin mata a Jamhuriyar Nijar

Gazali Abdou Tasawa
July 25, 2023

A Jamhuriyar Nijar, gwamnati ta ciwo bashin kudi daga Bankin kasashen Larabawa na raya Tattalin arzikin Afirka domin gina makarantun kwanan mata a wani mataki na bunkasa ilimi da kuma yaki da yi masu auren wuri.

https://p.dw.com/p/4UMuV
'Yan ta'adda sun tilasta rufe makarantu a Jamhuriyar Nijar
Makaranta a Jamhuriyar NijarHoto: Gazali Abdou/DW

Kudi miliyan 50 na Dalar Amirka ne gwamnati kasar ta Nijar ta ciwo bashi daga Bankin na BADEA domin gina makarantun kwana na ‘yan mata guda 50 a fadin kasar. Gwamnatin ta ciwo wannan bashi ne da nufin ci gaba da aiwatar da shirin Shugaban kasa Mohamed Bazoum na gina makarantun kwana na ‘yan mata guda 100 a fadin kasar da nufin bai wa ‘ya'ya matan damar yin karatun mai zurfi a cikin kykkyawan yanayi da kuma zai taimaka ga rage matsalar auren wuri da ake yi wa ‘ya'ya matan wanda ke tauye masu dama yin karatu. Malam Idi Harouna Daraktan kula da gine-gine a ma'aikatar ilimi ta kasa wanda ya tabbatar da cewa matakin yana da tasiri.

Jamhuriyar Nijar, Tillabéry | Shirin bunkasa makarantu
Makaranta a jihar Tillabéry da ke Jamhuriyar NijarHoto: Alliance Sahel/Aude Rossignol

Tuni dai kungiyoyin da ke fafutikar kare hakkin dan Adam da martabar ilimi a Nijar suka soma bayyana gamsuwarsu da yinkurin gwamnatin ta Nijar. Sai dai Malam Nassirou Seidou na kungiyar Muryar Talaka na ganin akwai bukatar sa ido wajen gudanar da wannan aiki. Ma'aikatar ilimin kasar ta Jamhuriyar Nijar ta ce a bisa kokarin da gwamnatin ke yi wajen gina makarantun kwana na mata a kasar ya sanya masu hannu da shuni suka shigo a cikin shirin domin bayar da taimako.

Yanzu haka dai tuni aka kaddamar da makarantar kwana ta mata ta farko da gwamnatin ta gina a cikin jihar Damagaram, makarantar da ke zama zakaran gwajin dafin shirin na Shugaba Mohamed Bazoum na inganta ilimin ‘ya'ya mata a kasar.