1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An binne Mugabe a mahaifarsa

Zainab Mohammed Abubakar
September 28, 2019

An dauki tsauraran matakan tsaro a daidai lokacin da iyalan tsohon shugaban kasar Zimbabuwe Robert Mugabe ke shirin binneshi a mahaifarsa ta Kutama

https://p.dw.com/p/3QPUq
Simbabwe Ex-Präsident Mugabe wird auf Helden-Friedhof beigesetzt
Hoto: AFP/T. Karumba

An tsara gudanar bankwana da ya kunshi 'yan uwansa da gayyatattun abokai, bayan kai ruwa rana na makonni da gwamnatin da ta tilasta Mugabe sauka daga mulki, dangane da inda za a binne tsohon jagoran da ya yi fafutukar samar wa da Zimbabuwe 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka na Birtaniya.

Baki da aka tantance ne kadai ke halartar jana'izar mutumin da akasarin al'ummarsa ke masa kallon "Gwarzon shugaba". Mai magana da yawun jam'iyyarsa ta ZANU-PF Simon Khaya Moyo ya bayyana rashin dacewar tsarin yi wa Mugabe bankwana ta karshen.