1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakan diflomasiyya don kawo karshen rikicin Siriya

April 14, 2012

Majalisar Dinkin Duniya za ta kada kuria a yau asabar domin tura jami'an sa ido zuwa Siriya don tabbatar da tsagaita wuta tsakanin sojojin gwamnati da 'yan adawa.

https://p.dw.com/p/14dv9
Bashar Ja'afari, Syria's ambassador to the United Nations, exits Security Council consultations at the UN in New York April 13, 2012. The U.N. Security Council moved quickly on Thursday in an effort to honor a request from international Syria mediator Kofi Annan to authorize the deployment of a U.N. truce-monitoring force to prevent a fragile ceasefire from collapsing. REUTERS/Allison Joyce (UNITED STATES - Tags: POLITICS TPX IMAGES OF THE DAY)
Hoto: Reuters

A yau kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya zai kada kuri'a kan dafatarin kudirin tura rukunin farko na dakarun soji zuwa Siriya wadanda za su sa ido wajen tabbatar da tsagaita wuta tsakanin gwamnati da mayakan tawaye. A ranar Alhamis din da ta wuce shirin tsagaita wutar da Kofi Annan ya gabatar ya fara aiki. A jiya juma'a wakilan kwamitin sulhun majalisar Dinkin Duniyar sun yi wata ganawa ta sirri na tsawon lokaci domin tattaunawa akan daftarin kudirin wanda Amirka da kawayenta na kasashen turai tare da kasar Rasha wadda ke zama babbar aminiyar Siriya suka tsara. Dukkan wakilan sun bukaci tura tawagar farko ta jami'an soji kimanin 30 domin share fagen tuntubar bangarorin biyu don tabbatar da tsagaita wutar ta kowane fanni tare kuma da mika rahoto ga kwamitin sulhun kan cigaban da aka samu na kawo karshen tarzomar. Sai dai kuma a waje guda rahotanni na cewa an yi musayar wuta a birnin Homs. 'yan adawa sun ce sojojin gwamnati sun yi luguden wuta a garuruwan Jouret al-Shiyah da kuma al-Qaradis, abin da ke yin barazana ga tsagaita wutar.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Saleh Umar Saleh