1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mataimakin Frime Ministan Masar ya yi murabus

October 11, 2011

Rahotanni sun ce mataimakin Frime Ministan Masar ya yi murabus sakamakon rashin gamsuwarsa da yunkurin gwamnati na shawo kan tarzomar da ta afku a karshen mako.

https://p.dw.com/p/12qKt
Mataimakin Frime Minista Hazem BeblawiHoto: picture-alliance/dpa

Mataimakin Frime Ministan Masar wanda kuma shine ministan kuɗin ƙasar ya yi murabus daga muƙaminsa domin nuna adawa da yunƙurin gwamnati wajen shawo kan tarzomar da ta afku a ƙarshen makon da ya gabata, wanda kuma ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutane 25, bisa bayanan da daya daga cikin na hanun damarsa ya bayar. Gidan talabijin na Masar ne ya fara rawaito wannan murabus na Minister Hazem el-Beblawi duk da cewa basu bayyana dalilansa na sauka ba. Su dai kristocin mabiya ɗarikar Coptic sun gudanar da wata zanga-zanga har ila yau a gaban gidan talabijin din dake alkahira. Gwamnatin rikon kwarya ta mulki Sojan kasar wadda ta fara jan ragamar mulki a watan Fabrairun da ya gabata ta yi alkawarin gudanar da sauye-sauye tun bayan hambarar da mulkin tsohon shugaba Hosni Mubarak to sai dai har yanzu dai ana cikin jiran tsammanin Warabbuka.

Mawallafiya: Pinado Abdu
Edita: Mohammad Nasiru Awal