1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Boko Haram ya tagaiyara dubban mata da yara

November 4, 2019

A shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya, kungiyoyin agaji da ke ayyukan jinkai sun ce akwai mata miliyan bakwai da rikicin Boko Haram ya tagaiyara, dake tsananin bukatar agajin gaggawa

https://p.dw.com/p/3SRy1
Nigeria | Flüchtlingslager in Pulko
Hoto: Getty Images/AFP/S. Heunis

Wadanna mata na fama da ukuba da yunwa da rashin samun kulawar likita ga rashin matsuguni, yanayin da ya jefa su shiga cikin yanayi mawuyaci. Kungiyoyin da ke aikin jin kai a shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya sun bayyana damuwa kan yanayin da matan ke ciki a inda su ka nemi hukumomi su kai musu dauki na gaggawa domin saukaka musu halin matsanancin rayuwa.

Malama Fanna Muhammad shugabar Kungiyar agaji ta Save Northeast Women wato kungiyar ceto matan shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya ta ce yanzu haka akwai mata da dama wadanda rashin muhalli ya sa su kwana a waje duk da yanayin damuna da ake ciki ga kuma sanyin hunturu da ke gabatowa. Wannan yanayi a cewar kungiyoyin ya tilasta wa mata da dama shiga karuwanci ko kuma yin bara tare da yin ayyukan bauta don samun abinda za su ci da kuma abinda za su taimaki rayuwar su.
Kungiyoyin sun kuma bayyana cewa ana samun mata da yawa na mutuwa saboda karancin kulawa ta lafiya inda ake samun hasarar raukan mata da yara wajen haihuwa. Duk dai da cewa akwai kungiyoyin da ke kokarin taimakawa dubun dubatar matan a kusan dukkanin jihohin Arewa maso gabashin Najeriya amma dai ayyyukan su ba sa wadarwa saboda yawan matan da ke cikin tsananin bukatar taimako.

Flüchtlingslager in Bama, Nigeria
'Yan gudun hijira a garin Bama a NajeriyaHoto: Reuters/S.Ini

A cewar Shehu Umar, wani mai fashin baki kan harkokin yau da kullum a Najeriya akwai bukatar gwamnati ta rubanya kokarin da ta ke yi ba kawai ta sa ido kan kungiyoyin jinkai na kasa da kasa daukar nauyin al’amuran matan ba. Dukkanin gwamnmatoci a jihohin Arewa maso gabashin Najeriya da ma gwamnatin tarayya na cewa suna bakin kokarin su wajen rage matsalolin matan musamman wadanda suka samu shiga sansanonin ‘yan gudun hijira da gwamnatocin ke kula da su.