1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu zaɓe sun bayyana gamsuwarsu da zaɓe a Masar

November 28, 2011

Ana gudanar da zaɓen ne na tsawon wkanaki biyu a ƙarƙashin tsauraran matakan tsaro da kuma zaman dirshan a dandalin Tahrir.

https://p.dw.com/p/13Ig4
Hoto: dapd

A yayin da ake ci gaba da kada kuri,u a zaben yan majalisar dokoki a kasar Masar, zaɓen da za a yi kwanaki biyu ana yinsa saboda halin tsaro a kasar, yawancin waɗanda suka kaɗa ƙuri,unsu sun bayyana gansuwarsu da yadda zaɓen ke gudana.

Zaɓen da shine zakaran gwajin dafin komawar ƙasar kan turbar demokiraɗiyya ya gudana cikin kwanciyar hankali.

Masu kaɗa ƙuri'ar da adadinsu ya kai miliyan sha bakwai da za su zaɓi wakilai sun gudanar da zaɓen nasu da farko cikin halin takatsantsan saboda rikicin da akai a ƙasar a satin da ya gabata wanda ya kai ga rasa rayukan fiye da mutane arba,in da jikkata ɗaruruwa, abin da ya kai ga wasu na kira da a ɗaga shi.

Mawallafi: Mahmud Yaya Azare
Edita: Mohammad Nasiru Awal