1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu zanga-zanga a Masar na nuna turjiya

August 12, 2013

Magoya bayan Mursi na ci gaba da nuna turjiya duk da barazanar gwamnati na kwashe su daga sansanonin da suke zaman dirshen da ƙarfi da yaji

https://p.dw.com/p/19OJK
Bildnummer: 60349564 Datum: 12.08.2013 Copyright: imago/Xinhua (130812) -- CAIRO, Aug. 12, 2013 (Xinhua) -- Protesters shout slogans in Raba a Al-Adaweya square where supporters of Egypt s ousted president have been sitting-in since June 28. Cairo, Aug. 12, 2013. Morsi s supporters prepared for a possible attack by security forces on their two main Cairo sit-ins in Al-Nahda square and Raba a Al-Adaweya square by building roadblocks and sand barriers. It comes as Egypt s leadership vows that the decision to disperse the sit-ins is irreversible. (Xinhua/Amru Salahuddien) EGYPT-CAIRO-PROTEST-SIT-IN PUBLICATIONxNOTxINxCHN Politik Protest x0x xsk 2013 quer Aufmacher premiumd 60349564 Date 12 08 2013 Copyright Imago XINHUA Cairo Aug 12 2013 XINHUA protesters Shout Slogans in Raba a Al Square Where Supporters of Egypt S ousted President have been Sitting in Since June 28 Cairo Aug 12 2013 Morsi S Supporters Prepared for a possible Attack by Security Forces ON their Two Main Cairo Sit ins in Al Nahda Square and Raba a Al Square by Building road blocks and Sand Barriers IT COMES As Egypt S Leadership Thatcher The Decision to The Sit ins IS irreversible XINHUA Egypt Cairo Protest Sit in PUBLICATIONxNOTxINxCHN politics Protest x0x xSK 2013 horizontal Highlight premiumd
Hoto: imago/Xinhua

Tsugune ba ta ƙare ba a taƙaddamar ikon da ke afkuwa tsakanin gwamnatin riƙon ƙwaryar Masar da magoya bayan hamɓararren shugaban ƙasar Muhammad Mursi.

A yau ma magoya bayan tsohon shugaban sun yi kira da a gudanar da zanga-zanga a duk faɗin ƙasar domin nuna adawa da shirin da gwamnati ke yi, na zuwa ta fatattaki waɗanda ke zaman dirshen a sansanonin da suka girka a babban birnin ƙasar wato Alƙahira.

Da bayyana wannan shiri na gwamnati, magoya bayan Mursin suka fara gina shingaye suna killace kansu a matsayin martaninsu ga barazanar da gwamnatin riƙon da Jami'an tsaron ƙasar suka yi.

A wani abin da ke nuna cewa barazanar ba ta ma yi tasiri ba, sansanonin sun ci gaba da samun ƙarin jama'a kamar ma ba su sami wannan sanarwa ba.

To sai dai ba a bayyane ya ke ba, ko a tsakanin 'yan kwanaki masu zuwa jami'an tsaro za su kara da magoya bayan Mursin.

Masu sanya ido dai na fargabar ta'azarar lamura, kasancewar masu zanga-zangar ko ɗaya ba su nuna alamar miƙa wuya ba, kuma sun haƙiƙance kan maida Mursi a matsayin shugaban ƙasa, zun bayan da aka tsige shi ran uku ga watan Yuli.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Saleh Umar Saleh