1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu boren Masar na nuna turjiya a dandalin Tahrir

November 21, 2011

Mako guda kafin gudanar da zabe masu boren Masar na cigaba da nuna turjiya a dandalin Tahrir da ke birnin Alkahira duk da jan idon da Jami'an tsaro ke yi musu domin tarwatsa su.

https://p.dw.com/p/13E7r
Hoto: DW

Sojojin Masar sun cinna wuta kan tantunan masu bore a dandalin Tahrir sun kuma harba hayaki mai sanya hawaye a wani yunkuri na tarwatsa dubun dubatan masu zanga-zangar neman gwamnatin rikon kwaryar sojin kasar da ta mika mulki zuwa ga fararen hula. Akalla mutane 11 suka hallaka a yayinda wasu da dama kuma suka jikkata. An kuma yi arangama a biranen da suka hada da Suez da Alexandiriya

Wannan ne rana ta biyu da shiga rikicin wanda ke kawo rudani a titunan kasar mako guda kafin gudanar da zaben farko tun bayan hambarar da gwamnatin tsohon shugaba Hosni Mubarak.

Tun Lahadi 'yan sanda da masu boren ke bata kashi kan tituna. Duk da cewa majalisar zartarwar kasar wacce ke samun goyon gwamnatin sojin ta yi alkawarin gudanar da zaben cikin lumana ran 28 ga wannan wata Nuwamba, masu boren na fargabar makomar zaben musamman ma fargabar cewa mukaraban tsohon shugaba Mubarak wadanda ke jamiyyar da ke mulki ka iya samun manyan mukamai. Bisa bayyanan wani jadawalin zaben da Jami'an sojin suka bayar, majalisar rikon kwarya zata mika mulki da zarar aka kammala zaben shugaban kasa daga karshen shekarar 2012 ko kuma daga farkon 2013

Mawallafiya: Pinado Abdu

Edita          : Abdullahi Tanko Bala