SiyasaJamus
Masu bore na bijire wa matakai a Sudan
October 28, 2021Talla
Kasashen duniya na ci gaba da nuna rashin jin dadi da zanga-zangar da ake fama da ita a Sudan, bayan hambare gwamnatin Firaministan kasar Abdallah Hamdok da Janar Abdel Fattah al-Burhan ya yi.
Masu zanga-zangar dai na ci gaba da fuskantar fushin jami'an tsaro ganin yadda suke bijirewa tare da datse hanyoyi.
Bayanai na cewa akalla mutum bakwai ne suka salwanta daga cikin wadanda ke furjanye wa gwamnati a tsakanin biranen Khartoum da kuma Omdurman.
Wasu rahotannin ma daga majiyoyin lafiya, na cewa ana samun karin wasu gawarwakin da ke dauke da alamun sara da kuma suka.
Bankin duniya tare da wasu manyan kungiyoyi da ma kasashe, sun sanar da dakatar da bai wa Sudan din tallafi, sakamakon abin da gwamnati mai ci ta aikata.