Masu adawan Siriya na cigaba da nuna turjiya
August 2, 2011Kwamitin Sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya ta gana da daren jiya a asirce domin tattauna ta'azaran da rikicin Siriya ke yi. Wannan ganawa dai ta biyo bayan rahotannin da suka fito daga Siriyan waɗanda ke zargin jami'an tsaron ƙasar da aikata kisar gilla a kan masu zanga-zanga. Masu fafutukar kare haƙƙin bil adama sunce aƙalla mutane 100 suka hallaka bayan da Jami'an tsaron suka kai hari da tankokin gwamnati ranar lahadi, a yayin da wasu bakwai kuma suka rasu a jiya litini. Shugabanin Tarayyar Turai da na daga cikin waɗanda suka yi kira da Kwamitin Sulhun da ya gudanar da wannan tattaunawar da fatar cewa ganawar zata kai ga ɗaukan matakan shawo kan rikicin da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa. Kawo yanzu dai mambobin kwamitin guda 15 sun kasa cimma matsaya dangane da matakin da ya kamata su ɗauka. A nasu ɓangaren dai masu boren nuna ƙyaman gwamnatin, sun sha alwashin gudanar da zanga-zanga a titunan ƙasar a kowani daren wannan wata na Ramadanan.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu
Edita: Umaru Aliyu