1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masoud Pezeshkian ya lashe zaben Iran

July 6, 2024

Rahotanni daga Iran na nuni da cewa, Masoud Pezeshkian na jam'iyyar masu ra'ayin kawo sauyi ya lashe zaben shugaban kasar.

https://p.dw.com/p/4hxTb
Masoud Pezeshkian ya lashe zaben Iran
Masoud Pezeshkian ya lashe zaben IranHoto: Vahid Salemi/AP/picture alliance

Masoud Pezeshkian ya samu nasarar lashe zaben kasar Iran da kuru'u miliyan 16, inda abokin karawarsa Saeed Jalili ya samu kuru'u miliyan 13 a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar Juma'a. 

Karin bayani: Ana gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu a Iran

Shugaban mai shekaru 69 da haihuwa da ke zama tsohon ministan kiwon lafiya ya yi alkawarin kawo gagarumin sauyi ga kasar a idon duniya. Sai dai duk wani buri da ake tsamannin ya zai kawo a siyasar cikin gida da ta kasashen waje, cikakken iko na zartar da komai na hannun jagoran juyin juya halin kasar Ayatullah Ali Khamenei.