1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masar za ta sa ido kan masu shiga Intanet

Yusuf Bala Nayaya
September 2, 2018

Shugaba Abdel Fattah al-Sisi na Masar ya rattaba hannu kan wata doka da ta ba da dama ga mahukunta su rika sanya idanu kan abin da al'umma ke yi a shafukan Intanet.

https://p.dw.com/p/34Anw
Ägypten Präsident al-Sisi
Shugaban Masar Abdel-Fattah al-SisiHoto: imago/ZUMA Press/Egyptian President Office

Tun a watan Yuli ne dai 'yan majalisa a Masar suka amince da kudirin dokar da za ta ba wa hukumar koli da ke lura da harkokin kafafen yada kabarai dama ta rika lura da abin da al'umma ke yi a shafukan intanet, musamman mutanen da ke da masu bin shafukansu da suka kai 5,000 a shafukan sada zumunta ko Blog ko kuma shafukansu na Intanet.

Wannan dai zai ba da dama ga wadanda aka ba wa alhakin lura da shafukan, su rufe ko dakatar da duk wani shafi da ya watsa labaran karya ko labarin da ka iya tada hankulan al'umma da haddasa rikici ko gaba tsakanin al'umma, ko kuma bata wa mahukunta rai.

Sai dai 'yan fafutika na kallon wannan doka a matsayin tarnaki ga mataki da ya yi saura a hannun al'umma da suke amfani da shi wajen bayyana abin da bai masu daidai ba a game da gwamnatin al-Sisi. Tuni ma dai tun kafin dokar ta fara aiki aka rufe wasu shafukan intanet kimanin 500.