1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masar ta sako 'yan jaridar Aljazeera

Gazali Abdou TasawaSeptember 23, 2015

Masar ta tsare 'yan jaridar ne bayan da kotu ta kamasu da aikata laifin nuna goyan baya ga jam'iyyar 'yan uwa musulmi da aka haramta a kasar.

https://p.dw.com/p/1Gc7w
Ägypten Mohammed Fahmy und Baher Mahmoud Al-Jazeera Journalisten
Hoto: picture-alliance/epa/K. Elfiqi

Hukumomin kasar Masar sun sako a wannan Laraba 'yan jaridar nan guda biyu na gidan talabijin na Aljazeera wadanda ke tsare a gidan kurkuku bayan da kotu ta kamasu da aikata laifin kawo goyan baya ga jam'iyyar 'yan uwa musulmi da aka haramta a kasar.'Yan jaridar Mohamed Fahmy dan asalin kasar Kanada mai shekaru 41 da abokin aikinsa Baher Mohamed dan kasar ta Masar dan shekaru 31 sun samu kansu ne bayan da Shugaban kasar Abdel Fatatah al-Sissi wanda ke fuskantar kakkausar suka daga kungiyoyin kare hakkin dan Adama, ya yi masu afuwa awoyi kalilan kafin ya tashi zuwa babban zaman taron Majalissar Dinkin Duniya da zai gudana a birnin New York.

A cikin watan Agustan da ya gabata ne wata kotun birnin Alkhahira ta yanke hukuncin zaman kaso na shekaru uku ukku ga 'yan jaridar a bisa zarginsu da bada labarin karya dama gudanar da aiki a cikin kasar ba tare da samun izini ba.