1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masar ta sake jadawalin zaben majalisunta

January 2, 2012

Shugabanin mulkin sojan kasar Masar sun sanar da gudanar da zaben majalisa gaba da wa'adi domin gaggauta mika mulki ga farar hula

https://p.dw.com/p/13cwg
An Egyptian man looks at a campaign banner in Arabic that reads, "The Freedom and Justice party," on the second day of parliamentary elections in Alexandria, Egypt, Tuesday, Nov. 29, 2011. Polls opened Tuesday for a second day of voting in Egypt's landmark parliamentary elections, the first since Hosni Mubarak's ouster in a popular uprising earlier this year. (Foto:Tarek Fawzy/AP/dapd)
Hoto: dapd

A matsayin martaninsu ga kiran da ake yi na gaggauta mika mulki ga farar hula sojojin Masar sun takaita lokacin gudanar da zabuka. A cikin wata sanarwa da ta bayar a birnin Alkahira babbar majalisar soji da ke mulkin kasar ta ce zaben majalisar dokoki ta biyu wato Shura yanzu zai gudana ne cikin watannin biyu a maimakon watannin uku tare da kawo karshensa a ranar 22 ga watan Fabarairu a maikakon 11 ga watan Maris. Bugu da kari ita majalisar ta shura za ta yi zamanta na farko ne wata guda gaba da wa'adi. To sai dai majalisun guda biyu ba za su iya kammala aiki akan sabon kundin tsarin mulkin kamar yadda aka shirya ba. Kuma har yanzu ana rashin sanin tabbas game da irin tasirin da 'yan majalisar za su ga tafarkin tsara dokokin. A dai watan Nuwamban shekarar 2011 ne aka fara gudanar da zaben mai zagaye da yawa da jam'iyar al-Ikhwanul al-Muslimun ta samu rinjaye a cikinsa.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Yahouza Sadissou Madobi