1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Masar ta kara bai wa kasar Somaliya manyan makaman yaki.

Suleiman Babayo MAB
September 23, 2024

A wannan Litinin ne wani jirgin ruwan kasar Masar karo na biyu dauke da makamai ya isa tashar jiragen ruwan kasar Somaliya, abin da ake gani zai iya kara zaman doya da man ja tsakanin kasashen da kuma Habasha

https://p.dw.com/p/4kyrb
Tashar jirgin ruwan Berbera ta Somaliya
Tashar jirgin ruwan Berbera ta SomaliyaHoto: Eshete Bekele/DW

Makaman da kasar ta Masar ta tura zuwa kasar ta Somaliya sun hada da manyan makaman soja masu cin dogon zango da makaman garkuwa. Tun farko wannan shekara ake kara samun karfafa dangantaka tsakanin kasashen Masar da Somaliya, inda duk kasashen suke da sabani da kasar Habasha. Ita dai Somaliya ta harzika saboda yadda Habasha ta kulla yarjejeniya da yankin Somaliland da ya balle daga kasar. Sannan ita kuma Masar ta fusata saboda yadda Habasha ta gina madatsar ruwa a kogin Nilo.