1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masar ta kama hanyar komawa bisa tafarkin dimoƙraɗiyya

September 18, 2011

Masar ta sanya ranar gudanar da zaɓukan majalisar dokoki a shirye-shiryen da take yi na komawa ga mulkin farar hula bayan juyin juya halin da ƙasar ta fuskanta

https://p.dw.com/p/12bV6
Boren daya kai ga kifar gwamnati a Masar.Hoto: dapd

Hukumomin ƙasar Masar sun ayyana 21 ga watan Nuwamba a matsayin ranar gudanar da zaɓukan majalisar dokokin ƙasar, kamar yadda tashar telebijin ta al-Arabiyya da kuma jaridar al-Ahram suka bayyanar. Wannan dai shi ne zai kasance zaɓe na farko tun bayan juyin juya halin daya kifar da gwamnatin tsohon shugaban ƙasar Hosni Mubarak cikin watan Fabrairu, bayan daya kwashe tsawon shekaru 30 yana mulki. Jaridar al-Ahram ta ƙasar Masar ta ruwaito cewar jefa ƙuri'ar zaɓen 'yan majalisar tarayyar ta ƙasar wadda aka fi sani da Majalisar al'umma, za'a gudanar da shi ne a matakai ukku, farawa daga 21 ga watan Nuwamba, da kuma kammalawa a ranar ukku ga watan Janairun baɗi.

Hakanan zaɓen 'yan majalisar dattijan ƙasar da aka fi sani da majalisar mashawarta ko kuma majlis al-shura kuwa, za'a farashi ne daga 22 ga watan Janairu, kana a ƙare a ranar 4 ga watan Maris. A cikin 'yan kwanaki masu zuwa ne ake sa ran hukumomin ƙasar ta Masar za su sanar da waɗannan ranaku - a hukumance. Sai dai kuma babu wata ranar da hukumoimin suka ayyana domin gudanar da zaɓen shugaban ƙasa.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu