1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masar ta fara toshe hanyoyin karkashin kasa zuwa Gaza

August 7, 2012

Bayan farmakin da ya yi sanadiyar mutuwar wasu dogaran tsaron kan iyaka a Masar, gwamnatin ta kudiri aniyar toshe hanyoyin karkashin kasa zuwa Gaza.

https://p.dw.com/p/15lRx
Members of the Egyptian forces repair a section of the breached border wall between Egypt and Rafah, in southern Gaza Strip, Monday Jan. 28, 2008. Egyptian security forces strung new barbed wire across one of the breaches in the border Monday in a sign that a six-day opening of the frontier may finally be reaching its conclusion.
Hoto: AP

Masar ta fara toshe hanyoyin karkashin kasa da ake fasakwaurin kayayyaki zuwa zirin Gaza kwanaki biyu bayan da wasu 'yan bindiga suka harbe sojojin Masar din 16 dake tsaron kan iyaka, harin da ake dora laifinsa akan 'yan takifen Falasdinawa. A waje guda dai jami'an Masar na nazarin matakin da za su dauka akan mummunan harin na yankin Sinai tsakanin Israila da Gaza. Tun bayan faduwar gwamnatin Mubarak watanni 18 da suka wuce sakamkon guguwar sauyi a kasashen larabawa ake ta samun yaduwar hargitsi a yankin kan iyakar. Rahotanni sun ce an tsaurara tsaro akan iyakar Rafah. Gwamnatin a birnin Alkahira ta ce 'yan bindigar da suka kai harin na ranar lahadi sun shiga Masar ne ta hanyoyin karkashin kasa. Ita ma Israila ta yi zargin cewa 'yan kungiyar Jihadil Islami na shiga Masar daga Gaza ta hanyoyin fasakwauri na karkashin kasa.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Yahouza Sadissou Madobi