Karin tsaro a tashoshin jirgin kasar Masar
May 13, 2018Talla
Jami'an tsaro suka ce baya ga matakan tsaro da aka kara, an kuma kame mutum 22 a tashoshi daban-daban na kasar ko dai daga bisani an saki da yawa daga cikin wanda aka kama din yayin da sauran da ke tsare da su ke ci gaba da amsa tambayoyi daga 'yan sanda. Hukumomi a kasar suka ce sun kara kudin jirgin ne don samun karin kudaden da za a fadada sufurin jirgin kasa a kasar sannan a samu sukunin kula da wanda ake da su yanzu haka.