1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al'umma sun fara juyawa shugaban kasar baya

Zulaiha Abubakar
September 27, 2019

Shugaba Abdel Fattah al-Sisi na Masar ya shaidawa magoya bayansa cewar su kwantar da hankalinsu game da zanga-zangar kin jinin mulkinsa bayan jami'an tsaro sun garkame kofofin shiga filin taro na Tahrir.

https://p.dw.com/p/3QN2N
Ägypten Regierungsfreundliche Kundgebung
Hoto: picture-alliance/dpa/M. el-Saied

An dai wayi gari da barkewar sabuwar zanga-zangar kin jinin shugaba Sisi a ranar 20 a wannan wata na Satumba ne sakamakon kiraye kirayen da ya karade kafafen sadarwar zamani a manyan biranen kasar. Da sanyin safiyar wannan rana shugaba Sisi ya koma kasar ta Masar daga birnin New York na kasar Amirka inda yake halartar babban taron Majalisar Dinkin Duniya.


Jami'an tsaro sun kame mutanen da yawansu ya kai dubu 1,900 tun bayan fara zanga zangar kin jinin shugaban kasar ta Masar a makon da ya gabata.