1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masar: Al Sisi zai yi mulki har zuwa 2030

Abdullahi Tanko Bala
April 16, 2019

Majalisar dokokin Masar ta amince da gyaran kundin tsarin mulki da zai baiwa shugaba Abdelfatah al Sisi damar cigaba da kasancewa a karagar mulki har zuwa shekarar 2030.

https://p.dw.com/p/3Guq5
Ägypten Parlamentssitzung
Hoto: AP

Gyaran dokar wanda za a gabatar da shi ga yan kasa don kada kuri’ar raba gardama na shan suka daga masu rajin kare dimukuradiyya wadanda suka baiyana cewa tamkar komawa ga mulkin kama karya ne shekaru takwas bayan juyin-juya hali da ya hambarar da mulkin shekaru 30 na Hosni Mubarak.

Yan majalisa 531 suka kada kuri’ar amincewa da daftarin yayin da yan majalisa 22 suka kada kuri’ar rashin amincewa dan majalisa daya kuma ya kaurace.

Kakakin Majalisar dokokin Ali Abdel Al yace wannan babbar rana ce ga kasar Masar.

Ana sa ran yan kasar za su kada kuri’ar raba gardama a farkon watan Mayu lokacin da musulmi za su fara azumin watan ramadan