1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin 'yan adawan Siriya

July 17, 2011

'yan adawan Siriya sun kafa sabuwar majalisar da zata ƙalubalanci Shugaba Bashsar al-Assad

https://p.dw.com/p/11wvu
Waɗansu jiga-jigan 'yan adawan SiriyaHoto: dapd

Masu faɗa a ji tsakanin waɗanda ke bijirewa gwamnatin Siriya, sun girka wata sabuwar majalisa wadda zata ƙalubalanci shugaba Basahr al-Assad. Mambobin adawan waɗanda mafi yawancin su na gudun hijira ne ko kuma sun ƙauracewa ƙasar sakamakon mulkin danniya da cin zarafin soji, sun gudanar da wani taro ne a birnin Istanbul a Turkiyya a jiya asabar. Masu fafutukan dai sun ce burin su shine su karɓi jagorancin ƙasar daga hannun shuga al Assad. A jiyan dai  masu adawan sun ɗage wani taron da  suka yi niyyar gudanarwa a wani gari mai suna Qaboon da ke kusa da Damascus bayan da aka yi zargin cewa jami'an tsaro sun hallaka wasu masu bore guda 14 wadanda suka halarci wani daurin auren da aka yi kusa da dakin taron da masu adawan suka yi niyyar gudanar da taron. Siriyan dai na cigaba da fama da tashe-tashen hankula na tsawon watanni da dama yanzu kuma shugaba Bashar al-Assad na fuskantar matsin ƙaimi daga alummar ƙasa da ƙasa, domin ya bar kujerar mulkin ƙasar.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu

Edita: Zainab Mohammed Abubakar