1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin Jamus akan Rasha da China

February 7, 2012

Dukkanin jami'an siyasar Jamus sun bayyana ɓacin ransu game da hawa kujerar na ƙi da Rasha da China suka yi dangane da ƙudurin kwamitin sulhu akan Siriya

https://p.dw.com/p/13ybS
TO GO WITH STORY MIDEAST SYRIA PROTESTERS BY ZEINA KARAM, In this citizen journalism image taken Tuesday, June 14, 2011, made on a mobile phone and acquired by the AP, Syrian women carry banners in Arabic that read:" Syria is for everybody, freedom, dignity, equality," " a shameful Arab League, stop being unfair,"" Russia and China, you are contributing in our killing," during an anti-regime protest in the Damascus suburb of Daraya, Syria. Bayan al-Bayasi, a 22-year-old student of Arabic literature had been steadily growing disillusioned with her president over the years, but like most Syrians raised on fear and submission, she kept silent. When the Arab protest wave reached Syria, she even defended Bashar Assad to her friends, saying she was sure he was a reformer at heart. It was her rising anger at the pictures of dead Syrians she saw every day on Arab satellite channels that drove her to join thousands of protesters packing a square on the Mediterranean coast. (Foto:Shaam News Network/AP/dapd) EDITORIAL USE ONLY, NO SALES, THE ASSOCIATED PRESS IS UNABLE TO INDEPENDENTLY VERIFY THE AUTHENTICITY, CONTENT, LOCATION OR DATE OF THIS HANDOUT PHOTO
Zanga-zangar adawa da Rasha da China a DamascusHoto: dapd

Bayan da a ƙarshen makon da ya gabata, ƙasashen Rasha da China, suka ɗare kan kujerar na ƙi domin hana wanzar da wani ƙudurin kwamitin sulhu na majalisar ɗinkin ɗuniya akan ƙasar Siriya, jami'an siyasa a birnin Berlin suka fara bayyana takaicinsu game da lamarin. Sai dai kuma har yau ana fatan samun sauyin salon tunani, aƙalla daga ɓangaren ƙasar Rasha. Jamus da Faransa suna fatan cewar ƙungiyar tuntuɓar junan da aka naɗa zata cimma nasara domin hana ci gaba da zub da jini a ƙasar ta Siriya.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta fito fili ta nuna cewar ba ma kawai takaicin hawa kujerar na ƙin na ƙasashen Rasha da China take yi ba, abin ma dai ya razana ta. Hawa kujerar na ƙi da gaggan ƙasashen biyu suka yi a ƙarshen makon da ya gabata, ta hana wanzar da ƙudurin dake Allah waddai da matakai na rashin imanin da ake ɗauka a Siriya. Bayan ganawar da suka yi da shugaba Sarkozy na Faransa a birnin Paris, Merkel tayi nuni da cewar:

Syrian President Bashar Assad, right, meets with Russian Foreign Minister Sergey Lavrov in Damascus, Syria on Tuesday, Feb. 7, 2012. Syrian forces renewed their assault on the flashpoint city of Homs on Tuesday as Russia's foreign minister held talks in Damascus with President Bashar Assad about the country's escalating violence. (AP Photo, pool)
Ministan harkokin wajen Rasha Lavrov na ganawa da shugaba AssadHoto: AP

"Abin da nike so na faɗa a nan shi ne, wajibi ne Rasha ta tambayi kanta da kanta ko shin nan gaba tana so ne ta zama wani abin misali na tarihi, inda zata riƙa bin manufofin da suka yi daura da na ƙungiyar haɗin kan Larabawa. Bana zaton hakan abu ne da zai cimma nasara. A saboda haka ba zamu dadara ba muna masu ba wa al'umar Siriya goyan baya da la'antar abubuwan dake faruwa a ƙasar."

Georg Streiter, mai magana da yawun shugabar gwamnatin a birnin Berlin ya fito ƙarara yana mai faɗa wa manema labarai cewar:

"Shugaba Assad bai cancanci ci gaba da mulkin ƙasarsa ba. Muna miƙa kira gare shi da ya share hanyar miƙa mulki a cikin ruwan sanyi. Ƙungiyar haɗin kan Larabawa ta tsara wani shiri wanda zai taimaka a fita daga mawuyacin halin da ake ciki yanzu a ƙarkashin wata gwamnati ta riƙon ƙwaryar da zata ƙunshi dukkan jam'iyyun ƙasar. Kamata yayi wannan shiri ya samu goyan bayan kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya, amma ba a hana wanzuwarsa ba."

A view of the Security Council as Vitaly I. Churkin, Permanent Representative of the Russian Federation to the UN, on behalf of his Government, vetoes a draft resolution strongly condemning the violence perpetrated by Syrian authorities against civilian protesters. The draft resolution was also vetoed by China, received nine votes in favour and four abstentions. Photo: United Nations/ Paulo Filgueiras +++(c) dpa - Bildfunk+++
Rasha da China sun hana wanzar da ƙudurin kwamitin sulhu akan SiriyaHoto: picture-alliance/dpa

Babban abin da ake fata shi ne, shawarwarin da ministan harkokin wajen Rasha Sergeij Lavkov zai gudanar a ziyararsa a birnin Damakus, su taimaka fadar mulki ta Mosko ta canza salon tunaninta, kamar yadda kakakin ma'aikatar harkokin wajen Jamus Andreas Peschke ya nunar. Tuni ma dai ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya ba da shawarar kafa wani kwamitin tuntuɓar juna da zai ƙunshi wakilan Majalisar Ɗinkin Duniya dake la'antar matakan gwamnatin Siriya da na ƙasashen Larabawa domin tattauna alƙiblar da za a fuskanta nan gaba. Su ma dai 'yan hamayya a Berlin sun bayyana ɓacin ransu game da kujerar na ƙin a New York. Shugabar jam'iyyar masu ra'ayin gurguzu ta Linke Gesine Lötzsch tayi kira ga gwamnati da ta gabatar da wani sabon ƙuduri a kwamitin sulhun na Majalisar Ɗinkin Duniya. Sai dai kuma ta ce bai kamata wannan ƙuduri ya ƙunshi wani mataki na soja kamar yadda lamarin ya kasance a Libiya ba. Ita ma Claudia Roth, shugabar 'yan the Greens ta kwatanta matakin na Rasha da China tamkar wata mummunar taɓargaza. Ta ce ga alamu ƙasashen biyu, ba maganar zaman lafiya da kwanciyar hankali ko girmama haƙƙin ɗan Adam ce ta dame su ba, maslaharsu ce kawai suka sa gaba.

Mawallafi: Betiona Marx/Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani