1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin Iran kan warware rikicin Siriya

May 10, 2013

Mahukuntan Iran sun ce sun yi na'am da matsayin da Amurka da Rasha su ka dauka na shirya taro a birnin Geneva da nufin warware rikicin kasar Siriya.

https://p.dw.com/p/18Vwp
Hoto: DSK/AFP/GettyImages

Mukaddashin shugaban kasar ta Iran Mohammad-Javad Mohammadizadeh ne ya bayyana hakan a wannan Juma'ar inda ya kara da cewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a shirye ta ke da ta bada gudumawarta yayin tarukan da nufin cimma burin da aka sanya a gaba.

Mr. Mohammadizadeh ya kara da cewar su na da tabbacin cewar in har an bi hanyar diflomasiyya yadda ya kamata to shakka babu za a iya warware rikicin cikin ruwan sanyi.

Iran dai na daga cikin kasashen da ke dasawa da gwamnatin Assad sosai, dalilin da ya sa kasashen duniya ke tallafawa dakarun gwamnatin da makamai a yakin da su ke yi da 'yan tawayen da ke kokarin kawo sauyin gwamnati.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Muhammad Nasir Awal