1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin gwamnatin Jamus game da masu kyamar baki

November 16, 2011

Ofishin ministan cikin gidan Jamus, ya bayyana aniyar daukar matakai domin dakile masu akidar kyamar baki

https://p.dw.com/p/13C4H
Hoto: picture-alliance / dpa

Ofishin ministan cikin gidan Jamus ya bullo da wani tsari na karfafa yaki da masu akidar kyamar baki ta 'yan nazi.Ministan cikin gida Hans-Peter Friedrich ya ce daga yanzu ofishinsa zai yi rijistar duk mutanen da ake zargin suna da iri wannan tsatsauran ra´ayi na kyamar baki domin daukar masu matakan ladabtarwa.

A wani jawabi da ta gabatar, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel , ta danganta kisan da a kayi wa wasu baki 'yan kaka gida dake Jamus a matsayin abin kunya ga Jamus.

Daga shekara 2000 zuwa 2006 masu akidar nazi sun kashe baki 'yan kaka gida su Tara, wanda suka hada da turkawa guda Takwas.

Gwamnati ta ce an samu kura-kurai ta fannin hukumomin tsaro wanda wajibi a magance su.

A yanzu haka wata sabuwar mahawara ta kabre a fagen siyasar Jamus, game da haramta jam´iyar NPD mai akidar kyamar baki.Tun shekara 2003 gwamnatin Jamus ta yi yunkurin soke wannan jam´iya, amma ta ci karo da adawa daga kotin koli.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Ahmad Tijani Lawal