Martanin Erdogan a kan boren 'yan Turkiya
June 3, 2013Firaministan Turkiya Racep Tayyip Erdogan ya zargi 'yan adawan kasarsa da iza wutar jerin zanga zangogin kin jinin gwamnati da suka barke a wasu sassa na kasar. Cikin wani jawabi da ya yi ta kafar telebijin a jiya lahadi da maraice, firimiyan ya ce ba abin da ya hadashi da salon mulkin kama karya da 'yan adawa suka zarge shi da gudanarwa.
Dubban 'yan Turkyia ne suka fara fantsaka a kan titunan birnin Istanbul kafin na sauran sassa su bi sahunsu, domin tilasta wa gwamnati lashe amanta game da shirinta na sabbin gine gine. Sai dai Erdogan ya danganta hanyar da suka bi wajen nuna rashin amincewarsu da yunkuri gurganta demokaradiya.
"Sun lalata abubuwa da dama tare da fasa tagogin wasu shaguna. Wai shin wannan ne demokaradiya? suka ce Tayyip erdogan dan kama karya ne. Idan ko suna kiran mutumin da ya sadokar da rayuwarsa wajen bauta wa kasarsa mai mulkin danniya, to ba ni da ta cewa."
Firaministan na Turliya Erdogan ya kuma kare jam'iyar da ke kan karagar mulki da zargin da ake yi ma ta na amfani da karfin ikonta wajen mayar da kasar kan tafarkin addinin musulunci tsantsa.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Saleh Umar Saleh