1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin ƙasashe akan boren Masar

February 1, 2011

Ƙasashen yammacin duniya sun fara nesanta kansu daga mulkin shugaba Hosni Mubarak na Masar da ke ci gaba da girgiza. saboda jajircewa da jama'a ke yi na ganin bayan mulkinsa na tsawon shekaru talatin.

https://p.dw.com/p/108hf
Sama da mutane miliyan ɗaya suka yi cincirindo don shiga zanga-zanga a birnin Alƙahira ranar talataHoto: picture alliance/dpa

Daidai da ƙasashen da suka daɗe suna mara masa baya kamar Amirka da kuma ƙasashen EU sun fara hannun riga da shugaba Mubarak. Ita dai ƙasar Amirka ta shiga sahun waɗanda suke matsa wa shugaba Hosni Mubarak lamba domin ya ɗauki matakan da za su ceto kimarsa a idanun talakawansa da ma ƙasashen duniya. Alhali ko da 'yan kwanaki ƙalilan da suka gabata, shugaban na Masar da 'yan ƙasarsa ke neman rabuwa da madafun iko, na zama ɗan lelen shugaba Obama da ma dai firaministan IsraIla Benyamin Netaniyahu saboda kai da ya ke ba su domin bori ya hau game da manufofinsu a rikicin yankin gabas ta tsakiya. A halin da ake ci yanzu haka dai, shugaba Obama na Amirka ya tura da manzonsa a ƙasar Masar domin ya fayyace wa Mubarak muhimmacin sadaukar da kai ga bukatun talakawa. Ko shi ma kakakin fadar mulki ta White House wato Robert Gibbs cewa yayi lokaci yayi da shugaba Mubarack zai kafa sabon tushe a mulkin kasar Masar:

Robert Gibbs Pressesprecher Weißes Haus
Kakakin fadar mulkin Amirka ta White House Robert GibbsHoto: AP

"Salon gudanar da mulkin Masar dole ne ya canza. Na yi imanin cewa za a yi sauye-sauyen da zai ɗora kasar kan kyakkyawar turba. Ba ƙasarmu ba ce, ko kuma gwamantin wannan ƙasa ba ce nauyin ya rataya wa a wuya."

Su ma dai ƙasashen Turai ba su fito fili sun bayyana cewa ba su juya wa Mubarak baya ba. Amma kuma suna ci gaba da yin jurwaye mai kama da wanka a inda suke nuna bukatar hanzarta gudanar da zaɓe mai inganci da zai buɗe sabon babin dangantaka tsakanin Masar da ƙungiyar tarayyar Turai. Wannan matakin dai ya saɓa wa wanda aka saba na shekaru gwammai da suka shafe suna yi da shugaban na Masar da ya shafe shekaru 30 a kan karaga. A lokacin wani taron ministocin harkokin wajen ƙasashen EU da ya gudana a birnin Bruselles, ministan harkokin wajen Jamus wato Guido Westerwelle ya ka da baki ya na mai cewa:

FDP Dreikönigstreffen Westerwelle
Ministan harkokin wajen Jamus Guido WesterwelleHoto: dapd

"Ƙungiyar tarayyar Turai ba za ta goya ma wani ɓangare baya ba. Amma kuma tana goyon bayan duk wani mataki da zai tabbatar da mulkin demokaraɗiya, zai kuma mutunta 'yancin faɗar albarkacin baki da kuma na kare haƙƙin bil Adam. Duk abubuwan da za su biyo baya, na cikin gida ne da 'yan Masar za su tattauna da juna a Masar domin warwaresu."

Koma dai yaya zata kaya dai, ƙasashen na yammacin duniya sun san cewa wanda zai maye gubin shugaba Mubarak nan gaba ba zai kasance ɗan bin yerima ba ne a sha kiɗa, saboda 'yan ƙasar na iya sabunta zangar-zangar har sai sun ga abin da ya ture wa buzu naɗi. Ko da shi tsohon shugaban hukumar makamashin nukuliya ta duniya, ya ke kuma riƙe da lambar yabo ta Nobel wato Mohammed El Baradei, wanda ake ganin ya fi dacewa ya shugabancin ƙasar, ya na samun saɓanin ra'ayi da ƙasashen yamma game da batutuwan da suka haɗa da takunkumin da suka ƙaƙaba wa Iran, da manufofin ƙasashen waje na Amirka da kuma uwa uba, sanya jam'iyar 'yan uwa musulmi na Masar da suka yi a rukunin masu tsaurin ra'ayin addini.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Ahmad Tijani Lawal