1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani kan koran soja a Masar

Usman ShehuAugust 13, 2012

Sallamar hafsoshin soji da shugaba Muhammad Mursi ya yi a ƙasar Masar ya samu maraba daga yan ƙasar

https://p.dw.com/p/15opi
In this photo released by the Egyptian Presidency, Egyptian Prime Minister Kamal el-Ganzouri, left, Field Marshal Hussein Tantawi, second left, President Mohammed Morsi, third left, and Chief of Staff Sami Anan, fourth from right, attend a ceremony at an Air Force base in in Cairo, Egypt, Tuesday, July 10, 2012. Egypt's Islamist-dominated parliament opened a new front in the country's leadership showdowns Tuesday by meeting in defiance of orders that disbanded the chamber and brought President Mohammed Morsi in conflict with both the powerful military and the highest court.(Foto:Fady Fares, Egyptian Presidency/AP/dapd)
Mursi a tsakiyan sojojiHoto: dapd

A wani mataki da ya dauka don kwatawa kansa cikakken ikon da majalisar sojin kasar Masar ta kwace masa tun kafin rantsar da shi, shugaba kasar Masar Muhammad Mursi, ya sallami shugaban rundunar sojin kasar, lamarin da ya jawo kace nace, tsakanin yan kasar.

Kasa da mako daya, bayan da Field Marshal Husain Tantawi ya yi rantsuwar kama aiki a matsayin ministan tsaron masar, shugaban kasar Muhammad Mursi ya sallame shi tare da manyan hafsoshin sojin kasar, a wani mataki dake kawo karshen sama da shekaru 60 na bararrajewar da sojoji suka yi kan al'amuran siyasar kasar.

A wani mataki da ya yi wa yan kasar ba zata, Mursi ya kara da rusa dokar da sojojin suka kafa wacce ta basu cikakken iko da zababben shugaba ke da shi, sai dai a wani jawabi da ya yi wa yan kasar, shugaba Mursi yace, bai dauki wannan matakin don ya musgunawa sojojin kasar ban e;

Field Marshal Mohamed Hussein Tantawi, head of Egypt's ruling military council, points to a painting as he accompanies Turkish Prime Minister Recep Tayyip Erdogan, not pictured, at the defence ministry in Cairo, Egypt, Tuesday, Sept. 13, 2011. Erdogan, intent on broadening Turkey's influence in the Middle East and the Arab world, started a visit to Egypt and will also visit Tunisia and Libya, two other countries where popular uprisings have ousted autocratic leaders. (AP Photo/Amr Nabil, Pool)
Field Marshall Mohammed Hussein TantawiHoto: AP

"Yaku al'ummar Masar, ku sani cewa, ban dauki wannan mataki don cin fuska ga wasu mutane ba, ko don tsangwamar wasu ma'aikatun gwamnati ba, na yi haka ne, don maslahar kasa, fatar da nakewa sojoji itace, su koma ga bakin aikinsu mai matukar daraja, wato bawa kasa kariya "

Wannan matakin da shugaban ya dauka, ya zo ne, bayan wani hari wasu yan bindiga da suka kai a yakin Sina dake makwabtaka da Isra'ila, hare-haren da ake zargin jami'an tsaron kasar ta Masar da sakaci wajen hana aukuwarsu.

Tuni dai shugaban ya maye gurbin shugaban rundunar sojin da Sa'eedel Sisi, wani matashin soja da ya jima yana kira ga sojoji da su dukufa kan ayyukansu na soja, su bar tsoma baki cikin sha'anin siyasa.

Attacks on Sinai checkpoints aftermath epa03344701 Egyptian army soldiers patrol the site of attack in which 16 soldiers were killed a day earlier in Rafah, Egypt, 06 August 2012. Media reports state that 16 Egyptian security forces were killed and seven others injured on 05 August when militants opened fire on a checkpoint and commandeered vehicles during a Ramadan fast in Rafah. Having hijacked the vehicles, they raced to the nearby Kerem Shalom/Karm Abu Salem crossing point on the Egypt-Israel-Gaza border. Egyptian authorities closed the border crossing with the Gaza Strip at Rafah indefinitely. EPA/AHMED KHALED +++(c) dpa - Bildfunk+++
Sojin Masar a bakin iyakar RafaHoto: picture-alliance/dpa

Yawancin masu fafutukar girka tsarin dimokiradiyya a kasar dai sun yaba da matakin da shugaban ya dauka.

"Muna daukar wannan mataki a matsayin juyin juya hali na biyu ne, wanda bayansa, shugaban kasa ya fita daga kangi dake masa dabai bayi, ko da yake ina zatan, makiya juyin juya halin da aka yi za su nemi mayar da hanun agogo baya"

A can dandalin Tahreer da kuma kofar fadar shugaban kasar, dubban masu nuna goyan bayansu da matakin shugaban kasar ne su ka yi masa caffa.

An Egyptian protester hangs an effigy representing Egypt's military ruler, Field Marshal Mohamed Hussein Tantawi, the head of SCAF, The Supreme Council of the Armed Forces, at Tahrir Square in Cairo, Egypt, Tuesday, Nov. 22, 2011. Egypt's ruling military moved up the date for transferring power to a civilian government to July next year and consulted Tuesday with political parties on forming a new Cabinet. But the major concessions were immediately rejected by tens of thousands of protesters in Cairo's iconic Tahrir Square threatening a 'second revolution.' (Foto:Ben Hubbard/AP/dapd)
Masu bore a Masar dake neman a hukunta tsaffin jami'an gwamnatin MubarakHoto: dapd

Ita kuwa, Fareda Nakkash, wata yar jam'iyaar adawa cewa ta yi matakin, wata shiryayyiya ce da shugaban ke aiwatarwa a kokarinsa na mayar da Masar ta zama ta yan uwa musulmi sak.

"An tara iko baki daya a wajen shugaban da sannu sannu yake rikidewa shugaban ina wani kan ba ni ba, ya hadawa kansa ikon zartarwa da ikon tsara dokoki, lamarin da ko shugaban kama karya Mubarak bai taba yi ba"

Ga dukkan alama, nada tsofin hafsoshin sojin da aka sallama a matsayin masu bashi shawara da shugaba Mursi ya yi, wata dabara ce ta kaucewa shiga kafar wando daya da sojojin da suka zama ala kakai ga jaririyar demokiradiyar kasar.

Mawallafi: Mahmud Yaya Azare

Edita: Usman Shehu Usman