1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani game da mamayar Abiye a Sudan

May 24, 2011

Gwamnatin kudancin Sudan ta bayyana mamayar da gwamnatin Shugaba Omar El-Bashir ta yi a garin Abiye da cewar abu ne da ya saɓawa doka, kazalika karan tsaye ne ga kundin tsarin mulkin ƙasar.

https://p.dw.com/p/11NRB
Tutar kudancin SudanHoto: picture alliance/dpa

Mninistan sadarwa da watsa labarai na kudancin Sudan Barnaba Marial Benjamin ya ce kutsen da gwamnatin Shugaba El-Bashir ta yi gami da girke sojojinta a garin na Abiye abu ne da ya saɓawa doka, tare da keta haddin kundin tsarin mulkin ƙasar. Ya kuma ƙara da cewar shiga yankin da su ka yi wani yunƙuri ne na takalar yaƙi da mutanen wajen.

"Wannan wani yunƙuri ne na yaƙi, gare mu wannan tamkar yaƙi ne wanda ba zai haifawa yarjejeniyar zaman lafiyar da mu ka cimma ɗa mai idanu ba. Muna fatan ƙasashen duniya da kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya su sa baki a lamarin tare da ba gwamnatin arewacin Sudan umarnin janye dakarunta daga yankin na Abiye."


Referendum Südsudan
Shugaba Salva Kiir na kudancin SudanHoto: AP

Mr. Benjamin ya ƙara da cewar idan kuma su ka yi kunnen uwar shegu game da wannan kira, to sai kuma a san irin matakin da za ɗauka nan amman dai mu na son duniya ta sani cewar ba za mu yi ramuwar gayya ba game da harin su ka kai.

"Mun cimma yarjejeniya ta zaman lafiya da su saboda, haka wanne dalili ne zai sa mu kai farfmaki yanki arewaci? Ko alama ba za mu sa dakarun mu su rama abin da aka mana ba don kuwa mun cimma yarjejeniyar zaman lafiya da su gaban kasashen duniya."

Karyata farmaƙin da aka kai wa sojojin Sudan

Da ya ke mayar da martani game da zargin da ake wa yankin kudanci na fara takalar arewacin ƙasar da yaƙi musamman ma dai farmakin da dakarun na kudaci su ka kaiwa wani jerin gwanon motoci da ke ɗauke da sojin arewacin a watan mayun da ya gabata kuwa ministan cewa ya yi ba gaskiya ba ne game da maganar da ake ta farmakin da aka ce sojin SPLA sun kai. Da farko dai babu ko sojan SPLA ɗaya a garin Abiye kuma na tabbata an gaskata hakan yanzu. Lokacin da sojin gwamnatin El-Bashir su ka shiga garin na Abiye sun sami SPLA? Dakarun kawai da ke garin na haɗin gwiwa ne da ke aiki a garin wanda bangarorin biyu su ka amince da su gami da dakarun Majalisar Ɗinkin Ɗuniya.


Polizeieinsatz gegen Demonstranten im Sudan
'Yan sandan Sudan lokacin da suke far wa 'yan kudancin SudanHoto: picture alliance / dpa

To baya ga watsi da wannan zargi da su ka yi, ministan ya kuma ce nan gaba za su ci gaba da tattaunawa da gwamnatin da ke iko da arewacin ƙasar da kuma jam'iyyar NCP domin ganin sun warware saurfan matsalolin da su ka yi saura duka dai da nufin samar da zaman lafiya mai ɗorewa tsakanin ɓangarorin biyu.Kazalika ya kuma bayyan cewar shirye-shirye na nan na cigaba na samun'yancin kan yankin nasu a farkon watn yuli kamar dai yadda aka tsara a baya.

"Ba shakka za mu samu wannan 'yanci da muke nema ranar tara ga watan yuli. Muna nan ma muna ta gudanar da shirye-shirye. Muna kuma cigaba da tattaunawa da ɓangaren su El-Bashir game abin da yai saura baya da aka kaɗa ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a. Har yanzu dai muna kan bakanmu na gani an warware matsalar Abiye kamar dai yadda ya ke a yarjejeniyar zaman lafiyar da mu ka cimma saboda haka ba wani abu da zai hana samun wannan 'yanci. Mutanen kudancin Sudan sun kaɗa kuri'arsu ta neman ta su ƙasar kuma an gudanar da wanna zaben ba tare da wani maguɗi ba ko tursasawa masu zaɓen. "

Mawallafi: Ahmed Salisu/ Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu