1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani ga Sakamakon Zaben Girka

June 18, 2012

Girka ta tsai da shawarar ci gaba da amfani da kudin Euro

https://p.dw.com/p/15HK9
An EU and a Greek flag fly in front of ancient Parthenon temple, in Athens, Sunday, June 17, 2012 as Greeks vote in the most crucial elections in decades. Greece voted Sunday amid global fears that victory by parties that have vowed to cancel the country's international bailout agreements and accompanying austerity measures could undermine the European Union's joint currency and pitch the world's major economies into another sharp downturn. (AP Photo/Petros Giannakouris)
Hoto: AP

Gwamnatin Jamus ta bayyana jin dadinta game da sakamakon zaben majalisar dokokin Girka da ya gudana jiya Lahadi. Shugabar gwamnati, Angela Merkel ta ce kenan kasar ta Girka za ta yi abin da ke zaman wajibi akanta a matsayinta na mambar Kungiyar Tarayyar Turai(EU). Ministan kudin Jamus, Wolfgang Schaueble ya kira sakamakon zaben a matsayin kuri'ar da za ta ba da damar ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen da ake bukata. Kungiyar Tarayyar Turai ita kuma ta nuna gamsuwarta da sakamakon zaben. Akan haka ne shugaban hukumar zartarwar kungiyar, Jose Manuel Barroso da shugaban majalisarta, Herman von Rumpoy suka ce inda su tsawwala wa Girka matakan da ya dace ta dauka domin gyara tattalin arzkinta da sun kansu ba su ji shi da dadi ba. Ita dai Kungiyar Tarayyar Turai so take kasar ta Girka ta dawwama a matsayinta na mamba mai amfani da kudin Euro. Hakazalika kasuwannin hada hadar kudade na Asiya da Turai sun yi armashi a dangane da wannan sakamako.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Abdullahi Tanko Bala