1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani ga harin NATO a Libiya

May 1, 2011

Harin da ƙungiyar ƙawancen tsaron NATO ta ƙaddamar akan gidan shugaban Libiya yana ci gaba da janyo martani daga sassa daban daban

https://p.dw.com/p/117EY
Wasu daga cikin jiragen NATO dake jefa makamai a LibiyaHoto: AP

Wani ɗan majalisar dokokin ƙasar Rasha da a mafi yawan lokuta ke bayyana ra'ayin fadar mulkin ƙasar ta Kremlin, ya yi tofin Allah tsine ga harin da ƙungiyar ƙawancen tsaron NATO ta ƙaddamar a ƙasar Libiya, wanda jami'an gwamnatin ƙasar suka ce ya yi sanadiyyar mutuwar ƙaramin ɗan shugaban Libiyar da kuma jikokin sa guda uku. A cewar Konstantin Kosachyov hujjoji na ƙara fitowa fili cewar manufar ƙungiyar ita ce kissar shugaba Gaddhafi.

Sai dai mai magana da yawun shugaban na Libiya ya ce ko da shike yana gidan yayin da aka ƙadamar da harin, amma bai sami ko da ƙwarzane ba:

" Shugaban dama Matar sa suna cikin ƙoshin lafiya, ba tare da sun sami ko da rauni ba. Akwai ƙarin mutanen da suka mutu sakamakon harin."

A martanin da Carmen Romero, mai magana da yawun ƙungiyar NATO a birnin Brussels ta yi kuwa cewa ta yi ƙungiyar na ƙaddamar da hare-hare ne akan abubuwan da sojoji ke amfani da shi - ba wai fararen-hula ko kuma ɗaiɗaikun mutane ba.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umaru Aliyu