1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martabar Scholz ta dawo a idanun Ukraine

Zainab Mohammed Abubakar M. Ahiwa
June 17, 2022

Duk da cewar ziyarar Olaf Scholz a Ukraine da nufin karfafa wa kasar gwiwa da fatan samun muhimman abubuwa ta yi tasiri, wasu na ganin ba abu ne mai yiwuwa cikin sauki ba.

https://p.dw.com/p/4Cs7m
Ukraine | Bundeskanzler Scholz in der Ukraine
Hoto: Natacha Pisarenko/AP/picture alliance

Cikin sharhin da maburiyar DW Rosalia Romaniec ta ta rubuta, ta ce shugaban Gwamnatin Jamus Olaf Scholz ne da kansa ya zuzuta batun ziyarar tasa zuwa birnin Kiev sosai, wanda mutane da yawa ke fargabar cewa tabbas akwai yiwuwar gazawa. "Ba zan shiga cikin jerin gwanon mutanen da ke yin gaggawar shiga da fita don samun damar daukar hoto ba. Idan na je, zai kasance ne game da abubuwa na zahiri," in ji shi cikin wata guda da ya gabata.

Scholz ya tafi birnin Kiev ne tare da wasu shugabannin kasashen yammacin Turai biyu, watau shugaban Faransa Emmanuel Macron da Firaministan Italiya Mario Draghi. Mutanen uku dai na wakiltar kasashe uku mafi karfin tattalin arziki da siyasa a nahiyar Turai. Isar su ke da wuya, shugaban Romania, Klaus Johannes mai wakiltar gabashin Turai ya tare su. Ko da yake ba su jima a kasar ba an dauki hotuna da yawa, kuma ana iya cewa ya fi ziyarar "shiga da fita" nesa ba kusa ba.

Tafiyar shugabannin yammacin Turan uku na da nufin aiki a matsayin alamar hadin kan Turai da Ukraine. Duk da haka, kamar yadda ziyarar ke da mahimmanci, yana kuma da muhimmanci su ukun zu gabatar da wani abu a zahiri, musamman Olaf Scholz na Jamus wanda dukkan idanu ke a kansa. Bayan fiye da kwanaki 100 na yaki, a karshe shugaban gwamnatin Jamus ya hau jirgin kasa na dare zuwa birnin Kiev, tafiyar da ta zama tamkar ita ce mafi muhimmanci a tarihinsa na zama dan siyasa.

Ukraine | Olaf Scholz, Emmanuel Macron, Mario Draghi und Klaus Iohannis besuchen Irpin
Hoto: Ludovic Marin/REUTERS

Abubuwa biyu ne dai mafi mahimmanci Ukraine din ke muradin samu. Watau da karin manyan makamai daga kasashen yammaci na Turai, da kuma amince wa kasar ta samu wakilci a cikin kungiyar tarayyar Turai. Dangane da batun makamai, sakamakon ya kasance mai gamsarwa ne kawai. Scholz ya yi alkawarin karin manyan makamai; amma bai ce komai game da lokacin aika su ba. Za a dauki lokaci mai tsawo, duba da cewar ana horar da sojojin Ukraine yanzu a Jamus.

Sai dai shugaban gwamnatin bai yi takaici ba a lokacin da aka zo kan batu na biyu wato na neman shiga kungiyar EU. A matsayinsa na shugaban kasa mafi karfin iko a cikin kungiyar kuma wanda ke da alhaki na musamman game da Ukraine, ya yi bayani karara: "Ukraine wani bangare ne na dangin Turai."

Da wadannan kalaman, Scholz ya dauki ragamar jagoranci wanda ya zame wajibi a kan shugaban gwamnatin Jamus a cikin irin wannan yanayin.

Ukraine Kiew | Treffen mit Wolodymyr Selenskyj, Olaf Scholz, Emmanuel Macron, Mario Draghi und Klaus Iohannis
Hoto: Ludovic Marin/AP/picture alliance

Tabbas tafiyar ba ta cika dukkan burin kasar Ukraine ba. Sai dai ya zama dole ta yi hakuri idan ana batun manyan makamai. Amma ga Shugaba Zelenskyy na Ukraine, ainihin sakon da aka gabatar a wannan rana ya zame mafi mahimmanci. Gabanin ziyarar, ya ce; "Abin da muke bukata daga Kansila Scholz shi ne tabbacin cewa Jamus na goyon bayan Ukraine." Babu batun sulhu idan ana batun dangantakar Jamus da Ukraine da kuma Rasha.

Scholz ya fahimci sakon, kuma goyon bayansa ga yunkurin Ukraine na shiga kungiyar EU na nufin cewa tafiyar ta yi nasara, kuma wannan ba karamin aiki ba ne. An dade ana kallon Olaf Scholz da Emmanuel Macron na Faransa a matsayin manyan masu nuna shakku a Turai. Yarjejeniyar birnin Minsk dai ta mutu, don haka ba zabi ba ne ga Zelenskyy na Ukraine. Sai dai fita fili da manyan kasashen uku suka yi tare da bayyana Ukraine a matsayin dangin Turai, wata sabuwar alkibla ce.