1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cimma yarjejeniyar huldar diplomasiyya

Zainab Mohammed Abubakar MAB
December 11, 2020

Isra'ila da Maroko sun cimma yarjejeniyar maido da huldar diplomasiyya a karkashin sa idon Amirka, wanda ya sa ta zama kasar Larabawa ta hudu da ta rungumi kasar ta isra'illa cikin tsukin watanni hudu.

https://p.dw.com/p/3mYYK
Bildcombo I Benjamin Netanyahu ,Donald Trump, König Mohammed VI

Marokon ta bi sawun Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain da Sudan, a matsayin wadanda za su ci gaba da alaka da Isra'ila, wanda ake gani yunkurin Amirka ne na yin taron dangin yakar Iran ta hanyar rage kaifin tasirinta a yankin Gabas ta Tsakiya.

A wani yunkuri na sauya matsayin Amirka, bisa ga yarjejeniyar shugaba Donald Trump ya amince da la'akari da cewar Maroko ce ke da 'yancin mallakar yankin yammacin Sahara, yankin da ke cikin rikici na gomman shekaru tsakanin Marokon da mayakan Polisario da ke da goyon bayan Aljeriya, wadanda kuma ke fafutukar neman 'yancin cin gashin kai.