1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Manufofin sabon shugaban kasar Somaliya

Sarah SteffenSeptember 11, 2012

Sabon shugaban Somaliya Hassan Sheikh Mohamud wanda ba shi da kwarewa a fannin siyasa ya fara nazarin hanyoyin magance rashin kwanciyar hankali kasarsa na shakaru 21.

https://p.dw.com/p/166lr
Residents walk past the campaign billboard of Somalia's presidential candidate Hassan Sheikh Mohamud in Somalia's capital Mogadishu, September 9, 2012. Somalia's lawmakers voted overwhelmingly on Monday for Mohamud as the country's next president, with the streets of the capital erupting into celebratory gunfire, Reuters witnesses said. Two of the four candidates who made it to the second round of voting opted out, leaving the incumbent President Sheikh Sharif Ahmed and Mohamud.Picture taken September 9, 2012. REUTERS/Feisal Omar (SOMALIA - Tags: POLITICS ELECTIONS)
Shugaba Hassan Sheikh na da jan aiki a SomaliyaHoto: picture-alliance/dpa

Shi dai Hassan Sheikh Mohamud ya zama zakaran da Allah ya nuna da cara a Somaliya ba tare da wani zato ko tsammani ba, saboda ba ya cikin rukunin 'yan takara da aka kyautata zato za su kai labari. Alalhakika ma dai shi sabon shugaban mai shekaru 56 da haihuwa, ya yi karatunsa ne a jami'ar Somaliya kafin ya zarce zuwa kasar Indiya inda ya samu digirinsa na biyu a birnin Bhopal a fannin kimiya da fusaha. Bayan da Hassan ya dawo gida a daidai lokacin da kasar ke daf da fadawa cikin rikici, bai mayar da hankali kan harkokin siyasa ba. Maimakon haka ma ya dogara ne kan harkokin ilimi inda baya ga karantarwa, ya fadakar a sassan Somaliya game da mahimmacin neman ilimi karkashin shirin UNESCO da kuma UNICEF. Hasali ma dai batun na alkinta zamantakewar manyan gobe tare da wadata su da ingantaccen tsari ilimi na sahun gaba na manufofin sabon shugaban na Somaliya.

Babban kalubale da Hassane Sheikh Mohamud zai fiskanta shi na cin hanci da karbar rashawa da ya yi katutu a cikin harkokin gwamnati. Sai dai lashe zagaye na biyu na zaben shugaban kasa da gagarumin rijaye da ya yi, ya bashi damar rike wuka da nama na hanyoyin magance matsalolin da ke ci wa somaliya tuwo a kwarya.

[25934732] Piraten in Somalia Ein Schnellboot der somalischen Küstenwache fährt mit schwerem Maschinengewehr am Heck am 27.03.2011 auf Patroullientour vor der Küste von Somalia. Zu wenig Boote, zu wenig Treibstoff, zu wenig Geld - trotzdem machen die rund 600 Mitglieder der Küstenwache von Somaliland Jagd auf die Piraten. Foto: Eva Krafczyk dpa (zu dpa Korr «Lösegeldzahlungen sind Küstenwachen-Admiral ein Dauer-Ärgernis» vom 17.07.2011)
fashi a teku ya zama karfen kafa a SomaliyaHoto: picture-alliance/dpa

Jabril Abdulleh da ke shugabantar cibiyar bincike da sassanta rigingimu da ke birnin Mogadischu, ya na daya daga cikin jami'an da suka shafe shekaru goma suna aiki tare da Hassan Sheikh Mohamud. Ya ce ko da shi ke ba a yi wani sanin sabon shugaban na Somaliya a duniya ba, amma dai zai yi amfani da gwamnatin da zai kafa wajen nuna irin alkiblar da ya doara kasara akai..

"Salon mulkin sa zai dogara ne akan irin mutumin da ya nada a matsayin firayi minista da kuma irin mutanen da majalisar zartarwar sa za ta kunsa, wadanda zai kira da suna majalisar gudanarwar da zai samar. Wannan ne zai nuna irin salon mulkin da zai tafiyar da kasar akansa."

Hassan sheikh Mohamud ya shafe shekaru ya na neman shawo kan 'yan al-Shabab domin su kwance damarar yaki a lokacin da ya ke aiki neman wanzar da zaman lafiya karkashin wata cibiya. Amma kuma masharhanta na ganin cewar da jan aiki a gabansa wajen dinke barakar da ke tsakanin haulolin kasar Somaliya da ke gaba da juna. Hakazalika bangare mafi girma na Somaliya na ci gaba da zama karkashin ikon masu tsattsauran ra'ayin addinin musulunci. Sai dai kamar tsohon shugaban wucin gadi, Hassan ya fito ne daga kabilar Hawiye da ke da angizo a Mogadischu babban birni. kana bai taba rike wani mukami na minista ko ma dai na dan majalisa ba. A cewar Laura Hammond, malama a kolejin koyar da al'adun Afirka da Asiya da le London ai sarki goma zamani goma ne.

Somali President Sheikh Sharif Sheikh Ahmed arrives to mark the first year anniversary since the ouster of militant Al Shabaab fighters from the capital Mogadishu August 6, 2012. REUTERS/Omar Faruk (SOMALIA - Tags: CIVIL UNREST POLITICS ANNIVERSARY)
Sharif Sheikh Ahmed ya rungumi kaddaraHoto: Reuters

"Tabbas abinda Hassan zai aiwatar a mukamin shugaban kasar Somaliya shi ne irin kyakkyawan sanin da ya ke da shi game da harkokin kasar inda yake zaune iya tsawon rayuwar sa. Kuma mutane na kiransa da suna babban malamin makaranta, abinda ya sa ya zama kwararren malamin da ya ke da masaniya akan lamuran siyasa. Hakanan ya shahara a fannin kungiyoyin da ke bayar da agaji. Saboda haka, mutum ne da ke da daraja a tsakanin rukuni daban daban na 'yan Somaliya."

A shekarar da ta gabata ne, Hassan sheikh Mohamud ya kafa jam'iyarsa ta siyasa wacce ba abin da ta sa a gaba illa ta ga cewar Somaliya ta zama tsintsiya madaurinki daya. Kuri'u 119 shi Hassan ya samu,yayin shugaba mai barin gado ya tashi da 79. Lamarin da Laura hammond ta kolejin koyar da al'adun Afirka da Asiya da ke London ta yaba.

"A gani na 'yan Somaliya da dama sun sami karfin gwiwar ganin irin ci gaban da aka samu a kasar. Abin mamaki ne ganin yadda majalisar dokokin kasar ta tashi tsaye domin samar da sabon sauyi. Wannan abin karfafa gwiwa ne sosai."

Tuni ma dai sabon shugaban na Somaliya ya fara amfani da facebook wajen mika sakon godiya ga 'yan kasarsa da ke ma'amala da wannnan kafa ta sadarwa.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Saleh Umar Saleh

Za a iya saurarar sautin wannan rahoton daga kasa