1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Manoma a Indiya sun bukaci karin farashi

Abdullahi Tanko Bala
March 14, 2024

Dubban manoma a Indiya sun yi gangami a Delhi babban birnin kasar suna neman karin farashi ga amfanin gonarsu.

https://p.dw.com/p/4dWTh
Indiya | Zanga zangar manoma
Hoto: Adnan Abidi/REUTERS

Zanga zangar manoman na zuwa ne wata guda bayan da suka yi sansani a arewacin kasar inda yan sanda suka dakatar da su daga shiga birnin na Delhi.

Karin Bayani: Zanga-zangar manoma na kara zafafa a Indiya

Wannan na faruwa ne yayin da ake sa ran nan da yan kwanaki gwamnatin ta Indiya za ta yi kiran sabon zabe da ake sa ran Firaministan kasar Narendra Modi zai sake neman tazarce a karagar mulki a karo na uku.