1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Maniyyata bikin Easter sun gamu da ajalinsu a Afrika ta Kudu

March 29, 2024

Rahotanni daga birnin Cape Towm a kasar Afrika ta Kudu sun sanar da mummunar hadarin mota da ya ta yi ajalin wasu mabiya addinin Kirista kimanin 45 da ke kan hanyarsu ta zuwa bikin Easter.

https://p.dw.com/p/4eFGT
Masu aikin neman gawarwakin mutanen da sukayi hadari a Afrika ta Kudu
Masu aikin neman gawarwakin mutanen da sukayi hadari a Afrika ta KuduHoto: eNCA/AP/picture alliance

Hukumomin yankin Limpopo sun tabbatar da afkuwar lamarin tare da bayyana cewa wani yaro daya 'dan shekara 8 kadai ya tsira da ransa a hadarin da a halin yanzu yake kwance a asibitin lardin.

Karin bayani:Azumi: kamanceceniyar dabi'u tsakanin Kirista da Musulmi 

Maniyyata bikin na Ista sun gamu da ajalinsu ne bayan motan ta fado daga kan wata gada daga bisani ta kone kurmus. Hukumomin yankin sun bayyana cewa motar ta taso ne daga makwabciyar kasar ta Afrka ta Kudu wato Botswana zuwa birnin Moria da ake gudanar da gagarumin bikin ibadar Ista a duk shekara.

Karin bayani: Bikin Easter a halin cutar coronavirus

Ko a bara, mutane sama da 200 suka mutu  adai wannan hanyar sakamakon hadarin da ke tattare da hanyar mai kwazazzabai da tsaunuka.