1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An amince da karbar bakin haure a Malta

Abdoulaye Mamane Amadou MNA
June 7, 2020

Hukumomi a tsibirin Malta sun amince da karbar bakin haure da 'yan gudun hijira da suka shafe tsawon makwanni kan teku sakamakon kin amincewa da su bisa fargabar cutar corona.

https://p.dw.com/p/3dOc4
Malta lässt nach Protesten 400 Migranten in den Hafen
Hoto: picture-alliance/dpa/J. Borg

Daukacin bakin hauren 425 an ceto su da jiragen agaji, kana sun fito ne daga kasar Libiya, a cewar wata sanarwa daga hukumomin Malta suka fitar. Tun daga farko tsibirin Malta ya bukaci wasu sauran kasashen Turai da su karbi wani bangare na daga cikin bakin hauren, lamarin da ya ci tura har kawo zuwa yanzu, abinda hukumomin tsibirin suka yiwa kakkausar suka.

Akalla bakin haure 3.405 ne suka sauka a tsibirin bayan sun ratso teku daga Libiya a shekarar bara, adadin da yanzu hakan wasu fiye da 2.790 ke ci gaba da kasancewa a tsibirin, kana daga farkon wannan shekarar zuwa yanzu akalla bakin haure 1.400 ne suka yi kasadar zuwa kan tsibirin daga Libiya.