1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta zargi Mali da neman hana ruwa gudu

Abdoulaye Mamane Amadou
July 21, 2022

Jamus ta zargi gwamnatin mukin sojan Mali da yunkurin hadasa tarnaki ga aiyukan rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya MINUSMA.

https://p.dw.com/p/4ETAz
Außenministerin Annalena Baerbock besucht Mali
Hoto: Florian Gaertner/Auswärtiges Amt/Photothek/dpa/picture alliance

Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock ce ta bayyana haka a yayin wata hira da tashar DW, tana mai cewa idan aka yi la'akari da jadawalin Minusma, fadar mulki ta birnin Bamako na kara dagula aiykan rundunar na wanzar da zaman lafiya da kare kungiyoyin agaji na kasa da kasa, tare da bayyana cewa  "Aikin rundunar Minusma a Mali shi ne na tabbatar da tsaro da kare ma'aikatan agaji na kasa da kasa kamar yadda Mali ta bukata. Na ziyarci Mali na kuma na tattauna da jama'a ciki har da matan da ke cewa burinsu shi ne su amu ko da zarafin zuwa kasuwanni don sayen kayan miya, amma hakan na faskara bisa rashin tabbatacen tsaro a garuruwa ko a yankunansu, yana da muhimmanci duniya ta kalli wannan batu."

Kalamun ministar harkokin wajen na Jamus na zuwa ne kwana daya bayan da gwamnatin Mali ta ba wa kakakin rununar Minusma sa'o'i 72 da ya fice daga kasar, bisa zarginsa da furta kalamun da suka sha bam-bam da manufofin gwamnati, bayan da ta kama sojojin Côte d'Ivoire 49 da Mali ta zarga da yi mata kutse.