1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindiga sun sace jagoran adawar Mali

Abdoulaye Mamane Amadou LMJ
March 27, 2020

Kawo yanzu babu masaniya kan inda jagoran adawar kasar Mali yake, bayan da wasu 'yan bindiga suka sace ce a kan hanyarasa ta zuwa Niafunké da ke yankin Timbuktu.

https://p.dw.com/p/3a8H1
Mali Präsidentschaftswahl 2018 | Soumaïla Cissé, Opposition
Soumaïla Cissé jagoran adawar kasar Mali Hoto: DW/K. Gänsler

Koda yake yankin na Timbuktu, yanki ne da 'yan ta'adda ke da karfi, sai dai kawo yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin yin garkuwa da madugun 'yan adawar kasar ta Mali Soumaïla Cissé. An dai halaka mai tsaron lafiyarsa guda an kuma jikkata wasu abokan tafiyarsa biyu, yayin da 'yan bindigar suka budewa tawagarsa wuta a kauyen na Niafunke, tare da yin awon gaba da da shi da kuma wasu abokanen tafiyarsa da dama. Hukumomin kasar Malin dai sun ce suna iyakacin kokarinsu domin gano inda aka shiga da madugun adawar. 

Mali na fama da matsaloli

An dai jima ana ta cece-kuce game da batun zaben 'yan majalisun dokoki da ake shirin gudanarwa a ranar Lahadi, duba da rashin tsaro da kuma kamarin yaduwar cutar Covid-19. Brema Ely Diko shi ne shugaban tsangayar kula da zamantakewar al'umma a jami'ar Bamako, a cewarsa an jima daman ana ta dage zaben na 'yan majalisun dokoki lamarin da ya sabawa ka'ida ta kundin tsarin mulki.

Mali neuer Präsident gewählt Ibrahim Boubacar Keita
Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar KeïtaHoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

A ranar 29 ga wannan watan ne dai hukumar zaben kasar ta ce za a gudanar da zaben na 'yan majalisun dokoki, sai dai da yawa daga cikin 'yan kasar hatta ma jam'iyyun siyasa na nuna dari-dari kan yadda Shugaba Ibrahim Boubacar Keïta ya nace akan sai an gudanar da shi, duk da matsaloli maras adadi da kasar ta Mali ta ke fuskanta. A zaben shugaban kasar da ya gabata Cisse ya sha kaye a gaban Shugaba Keïta koda yake ya ci gaba da nacewa akan matsayinsa na cewa ba a gudanar da zabe na gaskiya ba.