1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An ceto yan kasashen yamma a arewacin Mali

Abdoulaye Mamane Amadou
March 14, 2020

Hukumomi a kasar Mali sun gano wani dan kasar Italiya da 'yar kasar Kanada a yankin Kidal watanni 15 bayan da wasu 'yan ta'adda suka yi garkuwa da su a kasar Burkina Faso.

https://p.dw.com/p/3ZQcH
Mali Kämpfer der islamistischen Gruppe Ansar Dine
Hoto: Getty Images/AFP/R. Hien

Rahotanni daga yankin Kidal na arewacin Mali sun tabbatar da gano wasu 'yan kasashen yamma biyu da aka yi garkuwa da su tun a shekarar 2018 a kasar Burkina Faso.

Rahotanni sun ruwaito rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya da ke Mali MINUSMA na cewa dakarun rundunar sun gano mutanen biyu, daya dan kasar Italiyar Luca Tacchetto da 'yar Kanada Edith Blais ne a kusa da yankin Kidal a wannan rana ta Asabar, kana kuma tun a shekarar 2018 ce suke hannun masu tayar da kayar baya da makamai, suka yi garkuwa da su a cikin kasar Burkina Faso.