1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Malawi: Yabawar matasa kan soke zaben shugaban kasa

Kaliza Mirriam Umar Zaharaddeen/AAI
February 4, 2020

'Yan kasar Malawi na ci gaba da murnar soke zaben shugaban kasa da kotun tsarin mulkin kasar ta zartas a ranar Litinin. Kotun ta ce a gudanar da sabon zabe cikin kwanaki 150.

https://p.dw.com/p/3XGMN
Shugaban kasar Malawi yayin sa hannu a kotun kasar)
Shugaban kasar Malawi yayin sa hannu a kotun kasarHoto: picture-alliance/AP Photo

Bayan wannan umarnin na kotun, ta kara da cewa a mayar da tsohon mataimakin shugaban kasa kuma 'dan takarar shugaban kasa a zaben da ya gabata Saulos Chilima a mukaminsa har zuwa lokacin da za a gudanar da sabon zabe. 

Daruruwan matasa ne suka taru suna murnar wannan gagarumin hukunci da kotun tsarin mulkin kasar Malawi ta zartar. Kotun ta soke gaba daya zaben shugaban kasa da aka gudanar a watan Mayu na shekarar da ta gabata. Tun da farko hukumar zabe ta bayyana shugaba Peter Mutharika a matsayin wanda ya lashe zaben bayan da ya nemi yin tazarce. Wadan nan 'yan Malawi sun ce sun ji dadin yadda bangaren shari'a na kasar ya zartar da hukuncin ba sani ba sabo. Geoffry Kawanga na daya daga cikinsu da ya ke cewa:

Mr Lazarus Chakwera 'dan takarar shugaban kasa a Malawi kuma 'dan adawa
Mr Lazarus Chakwera 'dan takarar shugaban kasa a Malawi kuma 'dan adawaHoto: Getty Images/AFP/A. Gumulira

''Wannan lokaci ne mai muhimmanci a tarihinmu da kuma tarihin bunkasar dimukuradiyyarmu. Ina mai nuna farin ciki da yadda duk da munanan labarai da ake fadi a kan wannan shari'a, akwai jajirtattun mutane da ba su yarda wannan ya hana su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata ba.''

A yanzu dai kotun tsarin mulkin kasar ta bayar da umarnin a gudanar da zabe a cikin kwanaki 150. Sai dai kafin wannan lokacin shugaba Peter Mutharika zai ci gaba da kasancewa a matsayin shugaban kasa. Jam'iyyar adawa ta Malawi Congress Party ta ce tana fatan dan takararta na shugaban kasa shi ne yanzu zai lashe zaben da za a sake gudanarwa. Richard Chimwendo shi ne shugaban matasa na jam'iyyar wanda ya ce:
''Mun godewa alkalai a bisa yadda suka bamu nasara, sun yi kokari wurin tabbatar da gaskiya ta yi halinta. Muna masu godiya ga Allah ga wannan labari. Za ku ji cikakken bayani daga uwar jam'iyyarmu, domin yanzu duk inda ka duba kowa murna yake yi. Mun yi imanin cewa sai dan takararmu Dr. Lazrous Chakwera ya zama shugaban kasa sannan Malawi za ta fita daga cikin kangin talauci da rashin adalci.''

Ma'aikatan lura da ka'da kuri'a a a zaben kasar Malawi
Ma'aikatan lura da ka'da kuri'a a a zaben kasar MalawiHoto: AFP/A. Gumulira

Sakamakon zaben da kotu ta soke ya nuna cewa da kyar da gumin goshi shugaba Peter Mutharika ya kayar da wanda ya zo na biyu Lazrous Chakwera, a don haka jam'iyyar adawa ta Mr Chakwera ta MCP za ta ci gaba da cika bakin lashe sabon zaben da za a yi nan gaba kadan. Sai dai ga Dr. Mustafa Hussein wani mai sharhi kan al'amuran siyasa a jami'iar Malawi, hukuncin soke zaben da aka yi zai share fagen yin sahihin zabe a nan gaba. Ya ce watakila sai jam'iyyun siyasa sun yi hadin gwiwa kafin hakarsu ta cimma ruwa.


''Wannan abu ne mai kyau, 'yan Malawi na murna sosai. Domin dai yanzu dole a rinka martaba kuri'un da aka kad'a. Kuma hakan na nufin babu wanda zai kara sauya kuri'un jama'a, dole a bi doka. Hukumar da ke da hakkin gudanar da zabe ya zama wajibi ta bi tsarin mulki sau da kafa. Hukuncin ya zama babban darasi ga 'yan siyasa da cewa babu wanda yafi karfin doka. Yanzu 'yan Malawi sun yi nasara kuma dimukuradiyya za ta bunkasa a wannan kasa.''

Mr Lazarus Chakwera 'dan takarar shugaban kasa a Malawi kuma 'dan adawa
Mr Lazarus Chakwera 'dan takarar shugaban kasa a Malawi kuma 'dan adawaHoto: AFP/G. Guercia

Yayin da wasu mutane ke murnar wannan hukunci, kawo yanzu babu tabbas ko hukumar zaben kasar za ta daukaka kara zuwa kotun koli. Lauyan hukumar, Kalekeni Kaphale ya ce yana sauraron umarni daga hukumar zabe ko ya daukaka karar ko kuma su yi mubaya'a ga hukuncin kotun.
''Wannan na daya daga cikin hukunce-hukuncen da aka zartas, akwai sakamakon bincike, da mu da hukumar zabe za mu duba kafin mu sanar da mataki na gaba.''

Soke zaben shugaban kasar, ya sanya kasar Malawi ta biyo cikin kasashen da aka soke zaben shugaban kasarsu a Afirka a baya-bayan nan. A shekara ta 2017 wata kotun kasar Kenya ta soke zaben shugaba Uhuru Kenyatta. Sai kuma ga shi yanzu shugaba Peter Mutharika na Malawi shi ma kotu ta soke zaben da aka ce ya lashe a shekarar da ta gabata. Hukuncin da ke zuwa bayan da ya riga ya fara kafa sabuwar gwamnatinsa.