1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Malawi: An kama mataimakin shuaban kasa

Abdourahamane Hassane
November 25, 2022

An kama mataimakin shugaban kasar Malawi bisa zargin cin hanci da karbar rashawa dangane da bincike kan wata badakalar cin hanci da ta dabaibaye kwangilolin gwamnati da wasu manyan jami'ai suka yi.

https://p.dw.com/p/4K5qc
Shugaban kasar Malawi Lazarus Chakwera
Shugaban kasar Malawi Lazarus Chakwera Hoto: AMOS GUMULIRA/AFP

 

Hukumar yaki da  Cin Hanci da Rashawa  ta Malawi (ACB). ta cce Saulos Chilima ya karbi dalla dubu 280,000  daga  Zuneth Sattar dan Birtaniya mai asilin Malawi don samun kwangilar gwamnati. Hukumar ta ce 'yan sanda da sojoji sun bai wa wasu kamfanoni biyar na Mista Sattar kwangiloli 16 na dala miliyan 150, tsakanin shekarar ta 2017 zuwa 2021. Shugaba Lazarus Chakwera, wanda aka zaba bisa alkawarin yaki da cin hanci da karbar rashawa, ya tube mataimakinsa daga mulki a watan Yuni da ya gabata. Tuni dai aka kame wasu ministoci da tsaffin ministoci dangane da lamarin da ake zargin mutane da dama na da hannu a ciki