Makomar tawagar masu sa ido a rikicin Siriya
February 12, 2012Shugaban tawagar da Kungiyar Kasashen Larabawa ta tura a Siriya, wato Mohamad Ahmed Moustapha al-Dabi ya yi mubabus.
Cemma dai Moustapha al-Dabi, na shan suka daga kasashen ketare dangane da rawar da suka ce ya taka, a ta'asar da ta wakana a yankin Darfur na kasar Sudan.
Albakarcin taron na yau, kungiyar kasashen larabawa, za ta tattanawa game da yiwuwar fadada tawagar sa ido kasar Siriya, ga sauran kasashen da ma na musulmi ba.Wata mai magana da yawun gwamnatin Siriya ,Bassma Kodmani ta ce gwamnati ta amince da hakan:Wannan na matsayin zabi ga aikin komitin Sulhu na Majalisar Dinkin, tawagar za ta iya taimakawa a kawo karshen yakin ta hanyar hawa tebrin shawara tsakanin bangarori biyu.
To saidai kamin a kai ga wannan mataki, ana ci gaba da gwabza fada tsakanin dakarun gwamnati da sojojin da suka suka burjine mata.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Abdullahi Tanko Bala